‘Yan bindiga sun buƙaci fansar miliyan N20 ga kowane ɗan hidimar ƙasa da suka sace a hanyar Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

‘Yan bindiga da suka yi garkuwa da wasu ‘yan hidimar ƙasa (NYSC) kwanaki uku da su gabata sun nemi a biya Naira miliyan 20 ga kowane ɗaya daga cikinsu a matsayin kuɗin fansa, yayin da iyalai suka yi wa Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro majiyar a ƙoƙarta ceto su.

Rahotanni sun bayyana cewa masu hidimar ƙasar suna daga cikin fasinjojin da ke kan hanyar tafiya Abuja daga Jihar Bayelsa bayan kammala karɓar horon sati uku a sansanin NYSC da ke jihar, waɗanda aka yi awon-gaba da su a yankin babban titin Aloma zuwa Eganeda ke Ƙaramar Hukumar Ofu ta Jihar Kogi.

Wani ahalin ɗaya daga cikin ‘yan hidimar ya shaida wa manema labarai cewa masu garkuwar sun kira iyalan waɗanda aka sace sun faɗa musu buƙatarsu kan fansar, lamarin da ya tayar da sabon fargaba kan amincin ‘yan hidimar.

Wannan na zuwa ne bayan rundunar ‘yan sandan Kogi ta tabbatar da faruwar garkuwar wai fasinjoji ciki har da ‘yan hidimar ƙasar.

Rundunar ta bayyana cewa, an yi nasarar ceto mutane 11 ciki har da direbobin motocin biyu da aka sace bayan wani atisaye da haɗakar jami’an tsaro ta ƙaddamar.

By Babaji

Leave a Reply