
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Asabar Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi na II ya jagoranci hawan maulidi karo na farko a tarihin Masarautar Kano, yayin da dubunnan mutane suka taru don bikin murnar haihuwar Annabi Muhammad (SAW).
Sarkin ya je wajen taron ne da misalin ƙarfe 4:40 na yamma a sukwane kan dokinsa ta cikin unguwannin daɗaɗɗen birnin yayin da yake karɓar gaisuwa daga mazauna.
Sarkin ya fara tattakin nasa ne daga Ƙofar Kwaru sannan ya bi ta hanyar Mandawari zuwa Kwanar Ɗiso da Galadanci kafin zagaye yankunan Gwale, inda aka samu tarin dandazon jama’a na tarbar sa.
Ɗaya daga cikin ababen da suka ƙayatar a zagayen sarkin shi ne tsayawa akai-akai yana yi wa mazauna addu’o’i. Addu’o’in nasa sun mayar da hankali ne akan zaman lafiya, haɗin kai da ɗorewar al’amuran ci-gaba acikin al’ummar Jihar Kano.
