‘Yan bindiga sun sace basarake bayan halaka mutum uku da raunata biyar a sabon harin Kano

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

An halaka mutane uku, raunata wasu biyar da kuma garkuwa da Sarkin Noma na Jihar Kano, Alhaji Yusuf Nadabo Chiromawa a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki a garin Chiromawa da ke Ƙaramar Hukumar Garun Malam da ke jihar.

Al’amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na daren Asabar wayewar Lahadi, a cewar Shugaban Ƙaramar Hukumar Garun Malam, Alhaji Aminu Salisu Kadawa, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Kadawa ya ce, ‘yan bindigar sun kai wa yankin farmaki ne, inda suka je gidan sarkin noman kai-tsaye tare da buɗe wa jama’a wuta. A yayin haka ne suka halaka mutane uku yayin da wasu biyar kuma suka jikkata.

Ya bayyana cewa, waɗanda suka samu raunukan suna halin karɓar magani a wani asibiti, yayin da aka tura jami’an tsaro domin farauto maharan da kuma ƙoƙarin ceto basaraken.

Kadawa ya kuma ce, ya jagoranci ‘yan majalisarsa sun kai wa waɗanda aka raunata ziyara a asibitin da ake musu magani, inda suka kwana a can don tabbatar da an ba su kulawar da ta dace.

Ya ƙara da cewa, Gwamnatin Jihar Kano za ta ɗauki matakan tsaro a yankin don ganin irin haka bai sake faruwa ba.

Kazalika, shugaban ƙaramar hukumar ya kuma yi kira ga mazauna da su kwantar da hankali tare cigaba da kasancewa masu yin addu’o’i gami da bai wa jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar ba su bayanai masu amfani ga tsaron rayuka da dukiyoyinsu yayin da suke ƙoƙarin farauto maharan da ceto basaraken.

By Babaji

Leave a Reply