2027: KMT ne mafita ga Yobe – Hajiya Amina Amana

Spread the love

Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe

Fitacciyar ‘yar siyasa a Jihar Yobe, Hajiya Amina Amana, ta bayyana cewa Barrista Kashim Musa Tumsa (KMT) shi ne mutumin da ya fi dacewa ya jagoranci Jihar Yobe a matsayin gwamna a shekarar 2027, tana mai cewa al’ummar jihar za su amfana matuƙa idan aka ba shi dama.

Hajiya Amina ta bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ta yi da wakilinmu a lokacin da ta kai ziyara Jihar Gombe.

A cewarta, duk da cewa Barrista Kashim Musa Tumsa bai taɓa riƙe wani babban muƙamin siyasa ba, ya yi wa al’ummar Yobe ayyukan alheri da suka zarce na wasu da suka riƙe madafun iko.

Ta ce KMT na daga cikin masu neman tikitin takarar gwamnan Jihar Yobe a ƙarƙashin jam’iyyar APC, kuma ya cancanci a ba shi wannan dama saboda irin gudummawar da ya daɗe yana bayarwa ga jama’a.

“Shi ya sa nake mara masa baya. Na yi imanin idan Allah ya ba shi nasara ya zama gwamnan Yobe, talakawa za su ga sauyi na gaskiya a rayuwarsu,” in ji ta.

Hajiya Amina ta ba da misalin wata unguwa ta Rugar Fulani da ke ƙaramar hukumar Fune, inda ta ce mazauna yankin suka shafe shekaru suna neman a gina musu gada ba tare da samun biyan buƙata ba.

Ta ce, duk da cewa KMT ba ya rike da wani mukamin gwamnati, ya ɗauki nauyin gina gadar da kuɗinsa domin sauƙaƙa wa al’ummar yankin.

“A lokacin damina, mutanen yankin ba sa iya zirga-zirga, har yara ba sa iya zuwa makaranta saboda rashin gadar. Amma KMT ya magance wannan matsala da kansa,” in ji ta.

Ta kuma bayyana cewa KMT ya taimaka wa ɗalibai da dama wajen biyan kuɗaɗen makaranta, tare da haƙa rijiyoyin burtsatse a sassa daban-daban na jihar, ciki har da Machina, Nguru, Karasuwa da wasu yankuna domin samar wa al’umma ruwan sha mai tsafta.

A cewarta, a wani taro da KMT ya gudanar da al’ummar Lailai, bayan sun bayyana matsalar rashin ruwa da suke fuskanta, nan take ya ba da umarnin haƙa musu rijiyar burtsatse.

Ta ce idan KMT ya zama gwamna a shekarar 2027, mata da matasa za su kasance cikin manyan masu cin gajiyar gwamnatinsa ta hanyar samar musu da jari, horas da su sana’o’i da kuma shirye-shiryen dogaro da kai.

Hajiya Amina ta kuma yi kira ga al’ummar Jihar Yobe, maza da mata, matasa da manya, da su fito su sabunta katin zaɓensu domin su samu damar zaɓar shugabannin da suke ganin za su kawo ci gaba.

A ƙarshe, ta bayyana cewa tana da cikakken ƙwarin gwiwar KMT saboda yadda yake nuna kulawa da mutane ba tare da la’akari da matsayin su ba, tana mai cewa a shirye take ta ci gaba da wayar da kan mata domin mara masa baya a zaɓen 2027.

By ukarofi