
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A yau Lahadi Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja domin zuwa Nahiyar Turai don fara hutunsa na shekara mai tsawon sati uku.
Shugaban zai yada zango ne a Landon, Birtaniya, inda zai gudanar da wani kaso na hutun nasa. Kakakinsa Bayo Onanuga ne ya faɗi haka a wata takarda da ya fitar a ranar Lahadi, 30 ga Agusta, 2026.
A cewar sanarwar, shugaban ƙasar zai dawo Nijeriya ne bayan kammala hutun domin cigaba da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da za a fafata a Junairun 2027. Ya ce, Landon ne birni na farko da shugaban zai fara zuwa kana daga bisani ya he wasu wurare.
Haka na zuwa ne yayin da ake tsaka da harkokin gudanar da yaƙin neman zaɓe a babban zaɓen 2027 a matakai daban-daban tun daga kan shugaban ƙasa.
