Gwamnatin Nijar ta ce an samu kwanciyar hankali bayan boren sojoji a Niamey

Spread the love

Gwamnatin Nijar ta ce dakarun tsaron ƙasar sun daƙile wani hari da aka kai kan sansanin sojoji na Base 101 da ke birnin Niamey da wasu muhimman wurare a babban birnin kasar.

Ministan tsaron ƙasar, Janar Salifou Modi, ya ce maharan sun kai hari ne a wasu wurare masu muhimmanci a birnin Niamey, amma jami’an tsaro sun yi gaggawar mayar da martani.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, Janar Modi ya ce: “Gaggawar martanin jami’an tsaro da na tsaron kasa ya taimaka wajen dakile wannan yunkuri, tare da dawo da iko da wurin sannu a hankali.”

Ministan ya kuma ce, al’amura sun fara komawa daidai, yayin da jama’ar birnin Niamey suka ci gaba da gudanar da harkokinsu ba tare da wata matsala ba. “Al’umma kuwa suna cikin kwanciyar hankali, kuma suna ci gaba da gudanar da harkokinsu cikin ’yanci”, inji ministan.

Sanarwar wadda aka yaɗa a gidajen talabijin din ƙasar ta ce jami’an tsaro na ci gaba da tabbatar da tsaron muhimman wurare a babban birnin kasar.

Idan za a iya tunawa a watan Janairu wannan shekara ta 2026, Nijer ta fuskanci Makamancin irin wannan hari, wanda ya haddasa mutuwar sojoji da dama, sai dai an samu nasara daƙile shi bayan kashe gomman mahara.

By Babaji

Leave a Reply