Rasha ta taka gagarumar rawa yayin da sabon yunƙurin juyin mulkin Nijar ya tada ƙura

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Al’amarin rikicin sojojin Nijar ya sa an samu sabon yunƙuri dagula lamuran ƙasar, inda sojojin Rasha suke cigaba da taka muhimmiyar rawa, shekaru uku bayan Janar Abdourahamane Tchiani ya haye kan karagar mulki a wani juyin mulki.

Gwamnatin ƙasar ta ce sojojinta sun yi nasarar daƙile wani hari da aka kai kan sansanin sojoji na Diori Hamani International Airport, Air Base 101 da ke birnin Niamey da wasu muhimman wurare a babban birnin kasar a ranakun 28 da 29 ga Agusta.

Wannan al’amari ya janyo fargabar yunƙurin samun wani juyin mulki, yayin da wasu rahotanni suke nuna wasu mambobin sojojin ƙasar da suka yi bore sun kafa shinge a wasu yankunan babban birnin ƙasar.

Hukumomin ƙasar sun ce sojoji masu biyayya ga gwamnatin ƙasar sun daƙile wata tarzoma bayan sojojin da suka yi tawaye sun buɗe wuta a sansanin na Air Base 101. Rahotanni sun bayyana cewa, dakarun tsaron Nijar da haɗin-gwiwar sojojin Rasha sun yi nasarar daƙile wani harin da kuma kewaye fadar shugaban ƙasar daga wata barazana.

Ministan tsaron ƙasar, Janar Salifou Modi, ya ce an samu rahotannin da ke cewa wasu mahara sun ƙaddamar da hare-hare a wasu wurare masu muhimmanci a birnin Niamey, amma jami’an tsaro sun yi gaggawar mayar da martani.

Ministan ya kuma ce, al’amura sun fara komawa daidai, yayin da jama’ar birnin Niamey suka cigaba da gudanar da harkokinsu ba tare da wata matsala ba. Sanarwar wadda aka yaɗa a gidajen talabijin din ƙasar ta ce jami’an tsaro na cigaba da tabbatar da tsaron muhimman wurare a Niamey.

By Babaji

Leave a Reply