Duwan ya zama shugaban kwamitin shirin KT1T na shiyyar Daura

Spread the love

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, Ph.D., ya amince da naɗin Hon. Shafi’u Abdu Duwan a matsayin shugaban kwamitin shirin Katsina One-Person-One-Tree (KT1T) na shiyyar Daura.

Hon. Shafi’u Abdu Duwan zai jagoranci kwamitin shiyar wajen tabbatar da ingantaccen aiwatar da shirin dasa bishiyoyi miliyan 11 a yankunan da ke ƙarƙashin shiyyar Daura, tare da haɗa kai da ƙananan hukumomi, shugabannin gargajiya da na addini, mata, matasa da sauran masu ruwa da tsaki.

A matsayinsa na shugaban kwamitin, zai sa ido kan yadda ake aiwatar da shirin, wayar da kan al’umma kan muhimmancin dasa da kare bishiyoyi, tare da tabbatar da cewa bishiyoyin da aka dasa sun rayu kuma sun girma.

Shirin na da muhimmiyar rawa wajen yaƙi da kwararowar hamada, zaizayar ƙasa da sauran matsalolin da sauyin yanayi ke haifarwa, musamman a yankunan da ke fuskantar irin waɗannan ƙalubale.

Naɗin Hon. Shafi’u Abdu Duwan na daga cikin tsarin kwamitocin KT1T da gwamnatin jihar ta kafa domin tabbatar da ingantaccen gudanar da shirin a matakai daban-daban.

Mai bai wa gwamna shawara kan harkokin sauyin yanayi, Farfesa Al’amin Muhammad, shi ne ke jagorantar shirin a matakin jiha. A matakin shiyyoyi kuwa, Hon. Abdullahi Aliyu Turaji ne ke jagorantar shiyar Katsina, Hon. Shafi’u Abdu Duwan shiyar Daura, yayin da Hon. Iyaku Dabai ke jagorantar shiyyar Funtua.

A ƙarƙashin tsarin, shugabannin ƙananan hukumomi za su jagoranci aiwatar da shirin a ƙananan hukumominsu, yayin da kansiloli za su jagoranci shirin a mazaɓun su.

Ana sa ran Hon. Shafi’u Abdu Duwan zai taka muhimmiyar rawa wajen haɗa kan al’umma da tabbatar da nasarar shirin a shiyyar Daura, musamman wajen tabbatar da cewa dasa bishiyoyin ya wuce shuka kawai zuwa ga kulawa da su har su girma.

Gwamnatin Jihar Katsina ta tsara fara aiwatar da shirin KT1T a hukumance a faɗin jihar daga 10 ga Satumba, 2026, yayin da kwamitocin shiyyoyi da sauran kwamitocin da aka kafa za su ci gaba da shirye-shiryen wayar da kan jama’a domin ganin an samu nasarar shirin.

By ukarofi

Leave a Reply