
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Alhamis Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da Mista Abel Enitan Olumuyiwa a matsayin sabon Shugaban Ma’aikatar Ma’aikatan Tarayya (HoCSF).
Enitan ya maye gurbin Misis Didi Esther Walson-Jack, wadda ta yi ritaya bayan cimma shekarun yin ritaya na 60. An gudanar da ƙaramin taron rantsuwar ne a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, lamarin da ya yi sanadin fara wa’adin Enitan a matsayin shugaban ma’aikatan Nijeriya.
A ranar 19 ga Agusta ne Tinubu ya naɗa Enitan a muƙamin, a matsayinsa na mafi girma cikin manyan sakatarorin ma’aikatun tarayya.
Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Walson-Jack da mijinta Hon. Nimi Walson-Jack. Sai kuma matar sabon HoSCF, Misis Olawunmi Ololade Enitan; da kuma Babban Sakataren Fadar Mista Peter Fashedemi.
Shugaba Tinubu ya kuma taya Enitan murnar samun muƙamin gami da kira a gare shi da ya sauke nauyin da aka ɗora masa bisa ƙwarewa da tsare gaskiya da adalci.
A ranar 12 ga Disambar 1966 ne aka haifi sabon HoSCF ɗin. Ya yi digirinsa na farko a tsangayar harkokin banki daga Jami’ar Legas da na biyu a fannin Sharhin Tsare-tsaren Harkokin Al’umma daga Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi.
Haka kuma, ya shiga aikin gwamnati a shekarar 1998 a matsayin babban jami’in gudanarwa a ofishin Family Economic Advancement Programme (FEAP) da aka soke.

