Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin Ghana ta ƙi karɓar tallafin GH¢20 miliyan (kimanin Naira biliyan 2.4) da kamfanin MTN ya yi niyyar bayarwa domin tallafa wa ’yan Ghana da hare-haren kyamar baƙin fata suka shafa a Afirka ta Kudu.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Ghana ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, inda ta ce gwamnatin ƙasar ta riga ta tanadi isassun kuɗaɗe domin kwashe ’yan Ghana da abin ya shafa daga Afirka ta Kudu da kuma taimaka musu wajen komawa rayuwa bayan dawowarsu.
Ya zuwa yanzu, gwamnatin Ghana ta kwashe sama da ’yan kasarta 1,500 daga Afirka ta Kudu tun bayan barkewar sabon tashin hankalin kyamar baƙi a watan Afrilu.
Ma’aikatar ta ce gwamnatin Ghana tana yaba wa MTN bisa tayin tallafin, amma ta yanke shawarar ƙin karɓarsa.
A cewarta, gwamnatin ta riga ta sanar da shugaban hukumar gudanarwa da babban jami’in gudanarwa na MTN matsayinta a lokacin da suka gana da Ministan Harkokin Wajen Ghana, Samuel Okudzeto Ablakwa, a ranar 14 ga Agusta, 2026.
Gwamnatin Ghana ta kuma tabbatar da cewa za ta ci gaba da samar da tallafin jin ƙai da kuɗaɗen kwashe ’yan kasar da aka dawo da su daga wuraren da ke cikin haɗari.
Ta ce za ta bayyana wa jama’a cikakken bayanin kuɗaɗen da aka kashe wajen kwashe ’yan Ghana daga Afirka ta Kudu bayan kammala aikin.
