Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Mutum ɗaya ya rasa ransa, yayin da wasu mutane shida suka samu raunuka sakamakon wani rikici tsakanin matasan garuruwan Buskuwa da Mabani da ke ƙaramar Hukumar Gamawa a Jihar Bauchi.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta ce ta fara bincike kan lamarin, tare da kama wani mutum da ake zargi da hannu a rikicin.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Nafiu Habib, ya fitar ranar Alhamis, ya ce ’yan sanda sun samu rahoton lamarin ne ranar Laraba daga wani mazaunin ƙauyen Buskuwa mai shekaru 55.
Ya ce rikicin ya samo asali ne bayan wasu matasa uku daga Mabani da ke tafiya zuwa Buskuwa a ranar Litinin sun gamu da hari daga wasu matasa da ba a tantance ko su waye ba, waɗanda ake zargin ’yan Buskuwa ne.
Matasan, waɗanda aka bayyana sunayensu da Babangida Musa mai shekaru 20, Usman Abdu mai shekaru 20 da Ya’u Muhammad mai shekaru 18, an ce an lakada musu duka da sanduna, lamarin da ya jawo musu raunuka daban-daban.
Nafiu ya ce daga baya a wannan dare, wani mutum mai suna Jumba Adamu ya tattara wasu matasa daga Mabani domin kai harin ramuwar gayya zuwa Buskuwa, inda suka far wa mazauna garin da sanduna.
A sakamakon harin, wasu mazauna garin sun samu raunuka, yayin da Muhammadu Dare ya mutu nan take.
Bayan samun rahoton, jami’an rundunar ’yan sanda ta Gamawa tare da haɗin gwiwar mafarauta da ’yan sa-kai sun garzaya wurin da lamarin ya faru.
An kwashe waɗanda suka samu raunuka da gawar mamacin zuwa Babban Asibitin Gamawa domin ba da kulawar lafiya da gudanar da binciken gawar. Likitan da ya duba Muhammadu Dare ya tabbatar da mutuwarsa.
Rundunar ta ce mutane uku da suka samu raunuka suna kwance a asibiti suna karɓar magani, yayin da aka yi wa wasu mutum uku magani aka sallame su.
An kuma kama wani mutum da ake zargi da hannu a lamarin, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da ƙoƙarin gano tare da cafke sauran waɗanda ake zargin sun shiga rikicin.
Rundunar ta ce bayan kammala binciken farko, za a miƙa fayil ɗin shari’ar zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jiha (SCID) domin gudanar da cikakken bincike da gurfanar da waɗanda aka samu da laifi.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya yi Allah-wadai da rikicin, tare da umartar kwamandojin yankuna da jami’an ’yan sanda na sassan jihar da su ƙara amfani da dabarun sasanta rikice-rikice da sintiri bisa bayanan sirri domin hana sake ɓarkewar rikici.
Ya kuma yi kira ga shugabannin al’umma da mazauna Buskuwa da Mabani da su rungumi zaman lafiya, tare da guje wa ɗaukar doka a hannu.
Kwamishinan ya gargaɗi duk wanda aka samu da hannu a rikicin cewa zai fuskanci hukuncin doka, yana mai tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin jihar.
