Matatar Dangote ta ƙara farashin fetur duk da faɗuwar farashin ɗanyen mai

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Duk da raguwar farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya, Matatar Man Fetur ta Dangote ta ƙara farashin fetur, lamarin da ake sa ran zai sa farashin man ya koma kusan Naira 1,250 kan kowace lita.

Matatar Man Fetur da Sinadarai ta Dangote (FZE) ta ƙara farashin sayar da man fetur daga Naira 1,185 zuwa Naira 1,200 kan kowace lita. Sabon farashin ya fara aiki ne daga ranar 26 ga Agusta, 2026.

Rahotanni sun ce matatar ta sanar da abokan cinikinta da wannan sauyi ne ta wata sanarwa da sashen Ayyukan Kasuwanci na Rukunin Kamfanin ya fitar ranar Talata, inda aka bayyana sabon farashin man da ake lodawa daga tashar rarraba mai ta matatar da kuma farashin jigilar man ta teku.

A cikin sanarwar mai taken “Sanarwar Sauyin Farashin Fetur daga Naira 1,185 zuwa Naira 1,200 kan kowace Lita”, matatar ta umurci abokan cinikinta da su lura da sabon farashin fetur da aka tanada. Bayanin farashin da ke cikin sanarwar ya nuna cewa farashin man da ake jigilar wa ta teku ya tashi daga Naira 1,562,265 zuwa Naira 1,582,380 kan kowace metric ton, yayin da farashin da ake sayarwa daga tashar lodin matatar ya koma Naira 1,200 daga Naira 1,185 kan kowace lita.

Matatar ta kuma umarci masu sayen man da su dawo da dukkan takardun Izinin Karɓar Mai (ATC) domin a sake tantance farashinsu, sannan a ba su sabbin kwangilolin adadin man da za su karɓa domin a ci gaba da lodin mai nan take. Matatar ta ce hakan zai ba da damar ci gaba da loda man bisa sabon farashin da aka ƙayyade.

Wannan sabon ƙarin ya kai Naira 15 kan kowace lita, kuma ya zo ne kwanaki kaɗan bayan matatar ta ƙara farashin daga Naira 1,165 zuwa Naira 1,185. ƙarin farashin da ya gabata ya fara aiki ne daga tsakar daren 21 ga Agusta, 2026, kamar yadda masu bibiyar harkokin masana’antar man fetur suka bayyana. Abin da ya jawo cece-kuce shi ne yadda wannan ƙarin farashin fetur ya zo a daidai lokacin da farashin ɗanyen man fetur ke raguwa a kasuwannin duniya.

Bayanan Oilprice.com na ranar Talata sun nuna cewa farashin ɗanyen West Teɗas Intermediate (WTI) ya koma dala 82.13 kan kowace ganga, bayan ya faɗi da dala 2.88, wato kashi 3.39 cikin 100. Shi ma ɗanyen Brent ya koma dala 88.37 kan ganga, bayan ya yi asarar dala 3.80, kwatankwacin kashi 4.12 cikin 100. Haka kuma, farashin ɗanyen Murban ya faɗi zuwa dala 92.71 kan ganga, bayan ya ragu da dala 8.73, wato kashi 8.61 cikin 100.

Rahotanni sun nuna cewa ’yan kasuwar mai da masu sarrafa tashoshin ajiya da suka samu sanarwar matatar na iya fara mayar da tsoffin takardun ATC domin a sake tsara farashinsu bisa sabon umarnin.

ƙarin Naira 15 da matatar ta yi na iya haifar da ƙarin farashin fetur a gidajen mai, yayin da ’yan kasuwa za su ƙididdige kuɗaɗen sufuri, jigilar mai da sauran tsadar ayyukan rarraba man fetur. Saboda haka, ana sa ran farashin litar fetur zai koma matsakaicin Naira 1,250 a gidajen mai.

Har zuwa lokacin kammala rahoton, Matatar Dangote ba tya maida martani ga saƙonnin da aka aika masa domin jin ta bakinsa ba.

By ukarofi

Leave a Reply