2027: Yadda Bello Dalhatu ya fito da sabon tsarin ceton al’ummar Kano

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Dan takarar gwamnan Jihar Kano a ƙarƙashin jam’iyyar PDP a zaɓen 2027, Amb. Muhammad Bello Dalhatu, ya bayyana ƙudirinsa na sake fasalta tafiyar jihar, tare da mai da hankali kan bunƙasa tattalin arziki, samar da ababen more rayuwa da inganta rayuwar al’umma.

Amb. Dalhatu ya ce lokaci ya yi da za a kawo sauyi a Kano, yana mai cewa jihar na buƙatar shugabanci mai hangen nesa, ƙwarewa da kishin jama’a domin amfani da dimbin damar da Allah Ya hore mata.

Ya ce yana da burin samar da tsarin shugabanci da zai tunkari matsalolin da suka daɗe suna kawo cikas ga ci gaban jihar, tare da amfani da damar da Kano ke da ita ta fuskar albarkatun ɗan Adam, noma, kasuwanci da sauran ɓangarorin tattalin arziki.

Amb. Dalhatu ya jaddada cewa shugabanci nagari bai tsaya kan alkawuran siyasa da kalamai kawai ba, sai dai yana buƙatar ƙwarewa, sadaukarwa, jajircewa da kuma iya mayar da manufofi zuwa ayyukan da jama’a za su gani kuma su amfana da su.

Ya bayyana cewa yana da burin sake fasalta muhimman ɓangarorin jihar, samar da guraben ayyukan yi ga matasa, bunƙasa harkokin kasuwanci da inganta ababen more rayuwa domin ƙara ƙarfafa tattalin arzikin Kano.

Amb. Dalhatu ya kuma yi kira ga al’ummar Jihar Kano da su duba cancanta, ƙwarewa da tarihin hidimar ɗan takara wajen yanke hukunci a zaɓen 2027, maimakon dogaro da kalaman siyasa kawai.

Ya ce Kano na buƙatar shugabanci da zai haɗa jama’a wuri guda, ya saurari buƙatunsu, ya kare muradunsu tare da samar da mafita mai ɗorewa ga matsalolin da suke fuskanta.

Ya bayyana fatan samun goyon bayan al’ummar jihar domin aiwatar da wannan hangen nesa da kuma buɗe sabon babi na ci gaba a Kano.

By ukarofi

Leave a Reply