Hukumar bogi: ICPC ta zayyano manyan jami’an da suka taimaka wa Adeyemi bayan karɓar na goro

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ICPC, ta bankaɗo yadda aka zargi wasu jami’an gwamnati da taimaka wa Adeniyi Adeyemi, wato Darakta-Janar na hukumar bogi ta Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC) wajen samun wasu amincewa na gwamnati da damar shiga tsarin kuɗaɗe da gudanarwa a hukumance.

An bayyana haka ne a wani kundin rahoton binciken badaƙalar PFIPC na wucin-gadi da ICPC ta gudanar. Shugaba Bola Tinubu ne ya umarci a yi binciken bayan ayyana ƙungiyar a matsayin haramtacciya.

Bincike ya nuna cewa, ikon da PFIPC ta samun ya kai ga ta yi kutse cikin tsare-tsaren gwamnati sama da gabatar da takardun bogi da Adeyemi ya yi zuwa dogara da ayyukan wasu jami’ai da cibiyoyin gwamnati wajen amincewa akan wasu harkokin gudanarwarsu.

A cewar ICPC, Adeyemi ya fara neman amincewa ne a hukumance acikin tsare-tsaren gwamnati tun a Nuwamban 2024 a lokacin da ya nemi Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (OSGF) ya ba shi lambar shaidar gudanarwa, ikon gudanarwa na zaman kai da kuma amincewar buɗe asusu da Babban Bankin Nijeriya, CBN.

Daga cikin ababen da ya gabatar don amsa buƙatun nasa akwai takardar ɗaukar aiki, takardar samarwa da kuma takardar amincewar Fadar Shugaban Ƙasa, wanda ke zargin wani Akanbi Adewale ne ya sanya mata hannu. Hukumar da gano cewa babu wani mai suna Akanbi Adewale. Kuma binciken zaman ya nuna cewa Adeyemi ne da kansa ya sanya wa takardar hannu. Duk da waɗannan rashin gaskiya, an yi amfani da takardun wajen gudanar da aikin kan ababen da ya buƙata.

Haka kuma, daga bisani ICPC ta gano cewa Ofishin Akanta Janar na Ƙasa (OAGF) ya samar wa PFIPC bayanan tsarin gudanarwar kuɗaɗen gwamnati (GIFMIS) da asusun tara kuɗin gudanarwarta. OAGF ya kuma nemi CBN ya samar wa hukumar asusu guda biyu, waɗanda a cewarsa, an buɗe su amma ba su fara aiki ba, kamar yadda wakilin CBN ya shaida wa Majalisar Wakilai.

By Babaji

Leave a Reply