
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, ta ce ta kama wani babban ɗan kasuwa mai suna Innocent Ozoemena Ezuma bisa zargin sa da hannu a damfarar wani attajirin ƙasar Ukraniya wasu maƙudan kuɗaɗe har sama da Dala miliyan 120 a wani tsari da ake zargin ya kai kusan tsawon shekera 20.
Kakakin EFCC, Dele Oyewale ne ya tabbatar da kama Ezuma a wata takarda da ya fitar a ranar Talata, 20 ga Oktoba, 2026. Ya ce, an cika hannu da Ezuma mai shekaru 57 ne a Abuja a ranar Litinin, 19 ga Oktoba kuma yana tsare a ofishin hukumar. Ana tuhumar sa ne da zarge-zargen karɓar wasu kuɗaɗe da nufin damfara, cin amana, hirar aikata miyagun laifuka, karɓar kuɗi bisa bayar da bayanan ƙarya, sata da kuma sauya akalar kuɗaɗe.
A cewar bayanan da aka samu kan al’amarin, an kama mutumin ne bayan haɗin-gwiwa da masu bincike a matakin ƙasa-da-ƙasa da bayanan da wani mai fallasa acikin kamfaninsa ya bayar. EFCC ta yi zargin cewa, Ezuma ya amshi miliyoyin dalolin kuɗaɗe daga mai zuba jarin a tsakanin shekarar 2007 da 2015 domin gudanar da ayyukan albarkatun ƙasa da na lantarki waɗanda ba a aiwatar da su ba. An sauya akalar kuɗaɗe domin amfanin kai.
Haka kuma, hukumar ta fallasa wani zargi da ke nuna cewa an tura biliyoyin nairori acikin asusun kamfanoni da wasu mutane da aka danganta su da Ezuma, ciki har da ‘ya’yansa.
Masu bincike sun bayyana ɗansa mai shekara 28, Bogdan Ekene Ezuma, wanda ke gudanar da kamfanin Battregen Limited, a matsayin ɗaya daga cikin hanyoyin da ake sauya akalar kuɗaɗe. Sun ce daga Fabrairu zuwa Afrilun 2025, Bettregen ya karɓi lamunin kuɗi da adadinsu ya kai biliyan N1.365 duk da cewa babu wani kuɗin shiga da aka samu daga gare shi. Sannan, a Yulin 2025, an yi zargin an tura Naira miliyan 953 ga ƙaramin Ezuma, inda miliyan N90 ne kaɗai aka maido da shi.
Kazalika, masu bincike sun gano wasu hada-hadar kuɗaɗe na miliyan N48 zuwa miliyan N50 da aka tura wa asusun ‘yar Ezuma mai shekara 26, Bozhena Ezuma da wani ɗanuwa kuma abokin kasuwanci, Victor Ezuma. Sun gano cewa babu wani sahihin harƙallar kasuwanci da aka gudanar da kuɗaɗen.
A tsakiyar shekarun 2000s ne dai ake zargin Ezuma da yaudari wasu attajiran Ukraniya biyu wajen kiran su zuba jari a wani kamfanin ƙarafuna mai zaman kansa da ke Jihar Filato, Jos Steel Rolling Mill. Daga bisani ya karɓe iko da shi tare da sallamar ɗaruruwan ma’aikata ba tare da biyan su albshi ba. Bayanan da aka fitar, sun kuma nuna cewa Ezuma ya cigaba da zama a Nijeriya duk da cewa an sanya shi a sahun waɗanda ake nema ruwa-a-jallo.

