Tinubu ya maye gurbin Betta Edu da Mary Idele a kwamitin yaƙin neman zaɓen APC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cire tsohuwar Ministar Harkokin Jinƙai da Rage Talauci, Dakta Betta Edu a matsayin Daraktar Tattara Mata a Kwamitin Yaƙin neman zaɓensa na shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar APC (PBAT/APC/APC-PCC), inda ya maye gurbinta da Dakta Mary Alile Idele gabanin zaɓen 2027.

ADC-PCC ne ya sanar da sauyin tare da sanar da samar da cibiyar shiryawa, gudanarwa da gyare-gyare ga jagorancin cibiyoyin wayar da kan matasa da mata na kwamitin yaƙin neman zaɓen.

Sakataren ADC-PCC kuma Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma ne ya sanar da haka a wata takarda, ranar Talata. A ƙarƙashin sabuwar kwaskwarimar, an naɗa Dakta Farouk Adamu Aliyu a matsayin Daraktan Cibiyar Shirye-shiryen Matakai da Gudanarwa, yayin da Adejare Bello zai yi aiki a matsayin Darakta mai daraja ta biyu.

Haka kuma, kwamitin ya naɗa Ayo Olawande a matsayin Daraktan Wayar da kan Matasa da Dayo Israel a matsayin mataimakinsa. Ga ɓangaren wayar da kan mata, Dakta Mary Aille Idele ce Darakta, yayin da Betta Edu za ta yi mata mataimakiya, sai Hon. Imaan Suleman a matsayin sakatariya.

A cewar sanarwar, an yanke wannan hukunci ne bayan ƙaddamar da ADC-PCC kuma hakan na da nufin ƙarfafa tsare-tsaren shirin jam’iyyar da bunƙasa harkokinsa gabanin zaɓen na 2027.

By Babaji

Leave a Reply