Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Falmata, yarinya ce mai kimanin shekaru 16 zuwa 18 da ke karatu a wata makarantar sakandire ta ’yan mata a Jihar Borno. Wannan ita ce shekarar ta ƙarshe da za ta kammala karatun ta na sakandire, kuma tana da burin idan sakamakon jarabawarta na SSEC ya yi kyau za ta wuce zuwa jami’a don ta karanta aikin jarida a Jami’ar Maiduguri ko Jami’ar Bayero ta Kano. Sai dai wannan mafarki nata bai samu tabbata ba, saboda wani hari da ‘yan ta’adda suka kai wa makarantar tasu cikin wani mai ban tsoro.
A ƙarshe dai, Falmata ba ta samu damar cigaba da karatun ta ba, sakamakon garkuwar da ’yan ta’adda suka yi da su, a sansanin su da ke wani yanki na dajin Sambisa. Kodayake, ta samu damar tserewa daga sansanin ita da wasu ’yan mata su uku, bayan shafe tsawon watanni ba tare da gwamnati ko jami’an tsaro sun kai musu ɗauki ba.
Bayan ta koma gaban iyayenta a ƙauyensu da ke, mahaifinta ya kasa amincewa ta koma makaranta don ta ƙarasa karatun ta, saboda tsoro da fargabar abin da ka iya sake faruwa da ita. Don haka ya zaɓi ya aurar da ita ga wani ɗan amininsa da yake kasuwanci a Kano, domin ta yi nisa daga ƙalubalen tsaro dake addabar jihar su ta Borno da kuma yankin Arewa Maso Gabas bakiɗaya.
Kamar yadda ka karanta a labarin Falmata, wanda ƙirƙirarren labari ne, an tsara shi ne don ya zama misali ga irin yadda karatun yara mata ke fuskanta a yankunan da ke fuskantar matsalar tsaro a arewacin Nijeriya. Bincike ya tabbatar da cewa, akwai yara mata kimanin miliyan 23 da rayuwar karatunsu ta gurgunce sanadiyyar sace-sacen ’yan makaranta da garkuwa da ‘yan mata da ya zama ruwan dare a yankunan da ’yan ta’adda suke da ƙarfi.
A duk lokacin da aka yi garkuwa da wata yarinya daga makaranta, an nakasa ’yancinta ne, kuma an tauye mata haƙƙi, an ci zarafin ta, yadda rayuwarta ba za ta sake komawa daidai ba.
Fiye da shekaru goma kenan Nijeriya na fuskantar ƙalubalen tsaro, sakamakon ayyukan ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane. Daga Chibok zuwa Dapchi, daga Zamfara zuwa Kaduna zuwa Neja, ’yan ta’adda na kai hari cikin makarantu suna sace ɗalibai, musamman ýan mata. Idan sun yi sa’a an biya kuɗin fansa da wuri, su samu damar kuɓuta, ko kuma jami’an tsaro su yi sa’ar kai samame inda aka ɓoye su, su ceci rayuwar su. Sai dai abin takaici shi ne da dama daga cikin su ba sa komawa gida cikin hayyacinsu, ko cikin ɗiyaucinsu. Wasu ma a cikinsu har abada rayuwar su ba ta komawa daidai. Abu mafi ɗaga hankali shi ne lalacewar makomar karatunsu.
A yayin da aka gudanar da bikin ranar ’ya’ya mata ta duniya ta bana a ranar goma sha ɗaya ga watan Oktoba, masu ruwa da tsaki sun tattauna ne kan ƙalubalen cire yara mata a makaranta ana yi musu aure ba tare da sun kai shekarun da za su iya ɗaukar ɗawainiyar iyali ba. Yayin da kuma aka duba buƙatar tallafawa rayuwar yara mata don su inganta rayuwar su ta hanyar ilimi da sana’a. Kamar yadda muka bayyana a baya, tare da ba da misali a rayuwar Falmata, mun ga yadda waɗannan matsaloli suka firgita iyaye, har suke ganin kasada ce a bar yara mata a makaranta bayan sun fara zama ’yan mata don kada su faɗa mugun hannu.
A duk lokacin da ’yan ta’adda suka kai hari wata makaranta, farkon waɗanda iyaye ke cirewa a makarantar su ne mata. Iyaye a Borno, Kebbi, Zamfara, Neja da Kaduna, na ganin haɗari ne barin yara a makaranta saboda yawan hare-haren da ’yan ta’adda suke kai musu. Babban abin tsoron ma shi ne bayan sun kama su sun tafi da su, ba sa barin su haka, sai sun yi musu fyaɗe, sun lalata musu rayuwa. Wani lokaci ma har aurar da su suke yi a tsakanin su, saboda sun mayar da su ganima.
Bincike ya nuna cewa, a Jihar Borno kaɗai akwai yara dubu 700 da matsalolin tsaro suka raba su da makaranta, a cikinsu kashi 60 cikin ɗari mata ne. Bayan matsalar karatu da auren wuri, akwai matsalar ƙyama da firgici da yaran suke fuskanta ko da sun koma gaban iyayensu. Ana yi musu kallon lalatattu ko marasa amfani, ýan ta’adda sun gama da su.
Yana da muhimmanci jama’a su fahimci cewa waɗannan yara ba a son ransu ne aka ɗauke su ba, kuma ba a son ransu abin da ya faru da su ya faru ba. Idan an tausaya musu, an ja su a jiki, an tallafa musu, rayuwar su za ta iya dawowa daidai, har ma kuma su farfaɗo da rayuwarsu, su ba da gudunmawa ga al’umma, su kuma hayayyafa su samu iyali.
Sannan yana da kyau gwamnati ta fahimci cewa shirinta na ‘Safe Schools’ bai kamata ya tsaya ga samar da katanga da ajiye jami’an tsaro suna gadin bakin makarantu kawai ba. Ya kamata a samar da kyakkyawan tsarin da zai tallafawa rayuwar ɗalibai, yadda za su kula da kansu yayin da ’yan ta’adda suka kai wa makarantun su hari, ko tsautsayi ya sa sun shiga hannun ’yan ta’adda. A taimaka musu da dabaru na kare kai, neman ilimi daga gida, gina rayuwa ta fannin aiki ko sana’a.
Haka su ma iyaye, yana da kyau su fahimci cewa makomar rayuwar waɗannan yara tana ga Allah ne kuma tana gare su. Kada tsautsayin da ya same su a sa su barin karatu, ko kuma a tilasta musu aure da duk namijin da aka ga dama, ba tare da duba tarbiyyar sa, ko halayensa ba. Wani lokaci ma, kamar sadaka ake ba da su, babu wani sadaki kirki, ko biki na mutunci. Allah-Allah ake yi a rabu da ita, kamar wata mai mugunyar cuta.
Babban gatan da za mu yi musu a matsayin su na iyayen al’umma, ba aure ba ne. Abin da waɗannan ’yan mata ke buƙata shi ne, kulawa, jagoranci nagari, tattali, tarbiyya, da ilimantarwa. Kada mu ƙyamace su, kada mu guje su, kada mu wofintar da rayuwarsu. Mu nuna musu su ma ’ya’ya ne, kuma ana ƙaunar su. Mu tabbatar mun mayar da su makaranta, mun ba su kulawar da ta kamata, kafin mu ɗora musu ɗawainiyar iyali.
Haƙƙin gwamnati ne ta tabbatar ta shawo kan matsalolin tsaro dake addabar ƙasar nan, kuma ta tabbatar da ganin an kawo kƙarshen satar ’yan makaranta, da gurɓata musu rayuwa!
