Kotun ɗaukaka ƙara ta kori ƙarar Sahabi Ya’u a matsayin ɗan takarar APC na Zamfara ta Arewa

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Sakkwato ta yi watsi da ƙarar da Sanata Sahabi Ya’u Ƙaura ya shigar na ƙalubalantar hukuncin babbar kotun rarayya da ke Gusau, kan zaɓen fidda gwani na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na mazabar sanatan Zamfara ta Arewa.

A cikin hukuncinta, kotun ɗaukaka ƙarar ta tabbatar da hukuncin babbar kotun tarayya wanda Dakta Sani Abdullahi Shinkafi ya shigar, tare da tabbatar da umarnin gudanar da sabon zaɓen fidda gwani a mazaɓar.

Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan yanke hukuncin, lauyan Dr. Sani Abdullahi Shinkafi, Barista Bello Galadi, ya ce kotun ɗaukaka ƙara ta warware dukkan batutuwan da mai ɗaukaka ƙara Sanata Sahabi Ya’u ya gabatar kuma ta yi watsi da ƙarar saboda rashin hujja.

Barista Galadi ya bayyana cewa Sanata Sahabi Ya’u Kaura ya ƙalubalanci hurumin babbar kotun tarayya na sauraron shari’ar, amma kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hurumin ƙaramar kotun na sauraro da yanke hukunci kan lamarin.

Ya ƙara da cewa kotun ɗaukaka ƙarar ta kuma yi watsi da hujjar mai ɗaukaka ƙarar cewa ƙaramar kotun ta yi kuskuren juya wasu hujjoji, inda ta bayyana cewa an gabatar da isassun hujjoji a gaban kotun da ke tabbatar da rashin bin ƙa’idojin jam’iyyar APC na gudanar da zaɓen fidda gwani.

Ya bayyana hukuncin a matsayin gagarumar nasara ga dimokuraɗiyya da bin doka da oda, lauyan Dakta Shinkafi ya ce hukuncin ya nuna cewa babu wanda ya fi ƙarfin doka, ko da kuwa matsayinsa.

“Wannan hukunci ya tabbatar da matakin da wanda nake karewa ya dauka na neman adalci a kotu kuma ya aike da saƙo mai ƙarfi cewa rashin bin doka ba shi da gurbi a cikin tsarin dimokuraɗiyyar mu,” in ji shi.

Za a iya tunawa cewa Dakta Sani Abdullahi Shinkafi ya garzaya zuwa babbar kotun tarayya da ke Gusau, yana zargin cewa ba a gudanar da zaɓen fidda gwani na Zamfara ta Arewa ba kuma an samu kura-kurai a ciki.

Kotun ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Hussaini Dikko ta yanke hukunci a kan Dakta Shinkafi tare da umartar jam’iyyar APC da ta sake gudanar da sabon zaɓen fidda gwani cikin kwanaki 14. Rashin gamsuwa da hukuncin ne ya sa Sanata Sahabi Ya’u Kaura ya garzaya kotun ɗaukaka ƙara da ke Sakkwato.

Da yake martani kan hukuncin na baya-bayan nan, Dakta Sani Abdullahi Shinkafi ya bayyana hukuncin a matsayin nasara ga dimokuraɗiyya.

Ya kuma yi kira ga magoya bayansa da ke faɗin kananan hukumomin Shinkafi, Birnin Magaji, Zurmi da Kaura Namoda da suka haɗa Mazabar Sanatan Zamfara ta Arewa da su ci gaba da kasancewa cikin natsuwa tare da ci gaba da fafutukar samun wakilci na siyasa na adalci da nagarta.

By ukarofi

Leave a Reply