DSS ta gurfanar da mutum biyar kan sace ‘yan hidimar ƙasa 20 da wasu a Imo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS, ta gurfanar da wasu mutane biyar bisa zargin su da hannun a yin garkuwa da ‘yan hidimar ƙasa (NYSC) guda 20 da wani farin hula akan hanyar Owerri zuwa Onitsha da ke Jihar Imo.

An gurfanar da waɗanda ake zargin ne a gaban Mai Shari’a Oputa na Babbar Kotun Jihar da ke Birnin Owerri, bayan kama su a lokacin da aka ƙaddamar da wasu atisayen leƙen asiri a jihohin Ribas da Abiya.

Wasu ‘yan bindiga ne suka yi awon-gaba da mutanen a kusa da yankin Umunoha da ke Ƙaramar Hukumar Mbaitoli a ranar 1 ga Oktoba, 2026, a lokacin da suke hanyar tafiya daga Ibadan a Jihar Oyo zuwa sansanonin karɓar horon NYSC a jihohin Abia da Akwa-Ibom. Wannan al’amari ya sa jami’an tsaro suka ƙaddamar da atisayen bincike da nufin gano inda aka kai matasan da kuma kama masu hannu a ciki.

A ranar 7 ga Oktoba ne jami’an tsaro suka samu nasarar ceto ‘yan hidimar su 20 da wani mutum guda a dajin Amakohia-Ubi da ke Ƙaramar Hukumar Owerri ta Yamma. Daga bisani an ba su kulawar magani a asibitin DSS na Owerri.

Bayan wannan ceto ne sai DSS da haɗin-gwiwar sojoji da ‘yan sanda da wasu hukumomin tsaro, suka kama wasu mutane biyar yayin atisayen leƙen asiri da aka gudanar a tsakanin ranakun 10 da 14 na Oktoba a Fatakwal, Jihar Ribas da Aba a Abia.

Wasu uku daga cikin waɗanda ake zargin sun samu tserewa ɗauke da raunukan harbin bindiga, lamarin da ya sa aka ƙaddamar da atisayen farauto su domin gurfanar da su don su fuskanci hukuncin doka. Wannan mataki ne acikin binciken al’amarin garkuwar, yayin da aka fara shari’a akan mutanen da aka kama.

By Babaji

Leave a Reply