Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wata kotun tarayya da ta ke a Abuja ta saurari bayanin cewa, ƙungiyar ta’addanci ta ƙasa da ƙasa ta Al-ƙaeda ta taimaka wa ’yan ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru wajen kai hare-haren ranar 15 ga Mayu, 2026, kan wasu makarantu a ƙaramar Hukumar Oriire ta Jihar Oyo.
Shaidar ta bayyana cewa an kai hare-haren ne domin matsa wa Gwamnatin Tarayya lamba ta saki shugabannin ƙungiyar da aka kama, waɗanda Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ke gurfanarwa a gaban kotu.
Wani jami’in DSS da aka ɓoye sunansa, wanda aka bayyana da laƙabin “BBB”, ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da yake ba da shaida a matsayin shaida ta biyu a shari’ar wasu mutane biyar da ake zargi da hannu a hare-haren na Oriire.
Shaidar ta ce bayan sace ɗalibai da malamai a lokacin hare-haren, ’yan ta’addan sun miƙa wa Gwamnatin Tarayya jerin sunayen mutum 30 da suka haɗa da shugabanninsu da sauran mambobinsu, inda suka buƙaci a sake su ko kuma su kashe mutanen da suka yi garkuwa da su.
Mutanen biyar da ake tuhuma su ne Mahmud Muhammad, wanda aka fi sani da Abu Bara’a ko Abbas Mukhtar; Abubakar Abbas, wanda aka fi sani da Isah Adam ko Mallam Mahmuda Al-Nigeri; Abdulrazak Umar, wanda aka fi sani da Abu Khalifa ko Abu Khalid; Yunusa Musa, wanda aka fi sani da Abu Yunusa Bin Musa; da Shamsu Adamu Sani, wanda aka fi sani da Abu Itisar.
A cewar masu gabatar da ƙara, waɗanda ake tuhumar sun fito ne daga ƙaramar Hukumar Okene ta Jihar Kogi, ƙaramar Hukumar Daura ta Jihar Katsina da kuma ƙaramar Hukumar Suleja ta Jihar Neja. Shaidar, wadda Daraktan Masu Gabatar da ƙara na Tarayya, Oyedepo Rotimi, SAN, ya jagoranta wajen bayar da shaida, ta ce matakin da jami’an tsaro suka ɗauka domin ceto waɗanda aka sace ya biyo bayan ƙin amincewar Gwamnatin Tarayya na tattaunawa da ’yan ta’addan ko kuma biyan buƙatunsu.
Ya ce ya san waɗanda ake tuhumar ne ta hanyar aikinsa, musamman Mahmud Muhammad, wanda ya ce ya san shi a Maiduguri a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa ƙungiyar Boko Haram, kuma ya taɓa riƙe matsayin shugaban sashen tsaro da tattara bayanan sirri na ƙungiyar.
Shaidar ta ce Muhammad, wanda mahaifinsa ya fito daga Okene a Jihar Kogi, mahaifiyarsa kuma daga Jihar Borno, yana cikin waɗanda suka fice daga Boko Haram a shekarar 2012 suka kafa Ansaru. A cewarsa, manufar ƙungiyar ita ce yaɗa akidar kafa tsarin mulkin Musulunci a ƙasar da kuma kai hare-hare kan ’yan ƙasashen waje. Ya bayyana cewa mambobin ƙungiyar sun yi imanin cewa ’yan ƙasashen waje na kashe ’yan’uwansu Musulmi a wasu ƙasashe, lamarin da ya sa suka ɗauki matakin yin garkuwa da baƙi da kuma kashe su.
Shaidar ta ƙara da cewa kisan ’yan ƙasashen waje bakwai da ƙungiyar ta yi a shekarar 2014 ya sa Amurka ta ayyana Ansaru a matsayin ƙungiyar ta’addanci da aka haramta, tare da bayyana Muhammad a matsayin ɗan ta’adda da ake nema a duniya. A cewarsa, Muhammad ya jagoranci jerin ayyukan garkuwa da mutane da kisa bayan ya karɓi shugabancin Ansaru, yayin da Abubakar Abbas, wanda ake tuhuma na biyu, ya zama shugaban ayyukan ƙungiyar.
Shaidar ta ce Muhammad ya jagoranci harin da aka kai wa Sarkin Potiskum, inda aka kashe jami’an soji 17 da fararen hula uku a wani aikin da ya jagoranta. Ya kuma ce an kama Muhammad a shekarar 2025, kuma bisa akidar ƙungiyar, idan aka kama wani shugabanta, mambobi za su yi duk abin da za su iya domin ganin an sake shi.
Shaidar ta ce bayan kama Muhammad, Abbas ya zaɓi wasu manyan hare-hare da za a kai domin matsa wa gwamnati lamba ta sake shi. Ya ce a ranar 4 ga Nuwamba, 2025, ’yan ƙungiyar sun kai hari kan ayarin motocin wani ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Agwara/Borgu, Jafaru Mohammed Ali.
A cewarsa, an kashe jami’an soji huɗu, sannan jami’an DSS huɗu suka jikkata a harin. Shaidar ta ce manufar harin ita ce yin garkuwa da ɗan majalisar domin amfani da shi wajen tattaunawa da gwamnati kan sakin shugabannin ƙungiyar da aka tsare, ciki har da Muhammad da Abbas. Ya kuma bayyana cewa ’yan ƙungiyar sun shirya kai hari sansanin soji na Wawa da ke New Bussa, Jihar Neja, saboda sun yi zargin cewa a can ake tsare da wasu mambobinsu. Sai dai shirin bai yi nasara ba.
Bayan wannan yunƙurin, shaidar ta ce mambobin Ansaru sun koma yankin Kudu maso Yamma, inda suka yi imanin cewa za su iya amfani da gidajen yaɗa labarai wajen isar da saƙonsu da kuma ƙara matsa wa gwamnati lamba ta saki shugabanninsu da sauran mambobin da aka tsare. Shaidar ta ce yana daga cikin waɗanda suka gudanar da bincike kan sace ɗalibai da malamai a Oriire. Ya bayyana cewa bayan kai hare-haren, ’yan ta’addan sun kai waɗanda suka yi garkuwa da su wani wuri mai tsaro a cikin daji kusa da tsohon Gandun Dajin ƙasa na Old Oyo.
Ya ce masu garkuwar sun miƙa wa gwamnati jerin sunayen mutum 30, ciki har da shugabanninsu, tare da barazanar kashe waɗanda aka sace idan gwamnati ba ta biya buƙatunsu ba. A cewar shaidar, ’yan ta’addan sun nuna tsananin rashin tausayi, inda suka buɗe wuta kan jami’an tsaro lokacin da suka fara kai samame a dajin. Ya ce sun kashe ɗaya daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su tare da yin barazanar kashe sauran idan jami’an tsaro suka ci gaba da ƙoƙarin ceto su.
Shaidar ta ce bayan kashe mutum biyu daga cikin waɗanda aka sace, jami’an tsaro sun ga buƙatar ƙaddamar da aikin ceto, saboda suna sane da yadda ’yan Ansaru ke kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba. Ya bayyana cewa wani mataki da aka ɗauka shi ne kama matar Abubakar Abbas da wasu ’yan uwa na kwamandojin ƙungiyar da ke gudanar da ayyukanta a lokacin.
Shaidar ta ce an gargaɗi ’yan ta’addan cewa idan suka kashe wani daga cikin waɗanda aka sace, su ma za a kashe ’yan uwansu da aka kama. A cewarsa, wannan mataki ya taimaka wajen dakatar da kashe waɗanda aka yi garkuwa da su har zuwa lokacin da aka gudanar da aikin ceto. Ya sake jaddada cewa mutane biyu sun mutu kafin a ceto sauran waɗanda aka sace a harin na Oriire.
Yayin da yake bayanin yadda ya san mutum na uku, na huɗu da na biyar da ake tuhuma, shaidar ta ce dukkansu mambobin Ansaru ne da suke hulɗa da wasu kwamandojin ƙungiyar, musamman wani kwamanda da ke tsare da mutanen da aka sace a Oriire. Ya bayyana cewa hare-haren sun samo asali ne daga akidar da shugabannin ƙungiyar suka kafa, wadda ke buƙatar mambobi su kai hare-hare domin tilasta wa Gwamnatin Tarayya sakin shugabanninsu a duk lokacin da aka kama manyan kwamandojinsu.
Shaidar ta ce waɗanda suka shirya hare-haren Oriire sun yi ƙoƙarin matsa wa gwamnati lamba ta sake shugabanninsu, amma Gwamnatin Tarayya ta ƙi shiga tattaunawa da su. Ya ƙara da cewa ’yan ta’addan sun miƙa jerin sunayen waɗanda suke son gwamnati ta saki, ciki har da mutum na farko da na biyu da ake tuhuma, tare da barazanar kashe dukkan mutanen da suka yi garkuwa da su idan ba a biya buƙatunsu ba.
Shaidar ta ce jami’an tsaro sun yi nasarar ceto waɗanda suka tsira, amma aikin ya jawo asarar rayukan jami’an tsaro, ciki har da wani babban jami’in ’yan sanda da wani jami’in soji. Ya kuma tabbatar da cewa an kashe mutum biyu daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su kafin aikin ceton. An ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar Talata da ƙarfe 9 na safe a gaban Mai Shari’a Salim Ibrahim.
