Gwamnatin Tarayya ta fitar da ƙarin biliyan N4.04 don biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta fitar da ƙarin Naira biliyan 4.04 domin biyan haƙƙoƙin tsofaffin ma’aikatan Kamfanin Jiragen sama na Ƙasa (Nigeria Airways Limited, NAL) su guda 600, a matsayin wani ɓangare na biyan su bashin da suke bin tsohon kamfanin jiragen saman ƙasar.

Babban Mai taimaka wa Ministan Kuɗi kan harkokin yaɗa labarai, Maryann Duke ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, inda ya ce ‘yan rukunin 010 da 011 ne za su amfana da biyan na yanzu. A cewar sanarwar, wannan mataki ya nuna yadda gwamnatin take ƙoƙarin cigaba da sauke nauyin haƙƙoƙin tsofaffin ma’aikatan da aka tantance.

Wannan ya biyo bayan sanar da ware Naira biliyan 18 a watan Satumba, 2026 ga tsofaffin ma’aikatan kamfanin guda 2,700 daga rukuni na ɗaya zuwa na tara. Ma’aikatar Kuɗin ta bayyana cewa an shirya biyan kuɗaɗen ne a tsarin rukuni bayan rukuni bisa ga yadda aka tantance su da kuma rahotonsu domin tabbatar da cewa kuɗaɗen sun kai ga waɗanda aka ware domin su.

Sannan, ta ce gwamnatin ta yi la’akari da tsawon lokaci da tsofaffin ma’aikatan da iyalansu suka ɗauka suna jira da kuma warware matsalolin sahihan iƙirarin basussuka ta hanyar da ta dace tare da tabbatar da gaskiya da adalci, yayin da kuma ake ƙoƙarin bai wa dukiyar al’umma kariya ta hanyar tantancewa da doka ta tsara.

Kazalika, ma’aikatar ta ce za ta cigaba da goyon bayan aiwatar da nauye-nauyen da ke kan gwamnati bisa biyayya ga dokoki da hanyoyin biya da aka amince da su.

By Babaji

Leave a Reply