Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya bayyana cewa gwamnatinsa na da burin dasawa da kuma kula da bishiyoyi miliyan 11 a faɗin jihar kafin shekarar 2030, inda za a fara da bishiyoyi miliyan biyu a shekarar 2026, ƙarƙashin shirin Katsina-One-Tree Initiative (KT1T).
Gwamna Raɗɗa ya bayyana hakan ne a ranar yayin ƙaddamar da shirin Katsina-One-Tree Initiative (KT1T) a Ladanawa, ƙaramar hukumar Rimi. Shirin ya shafi dukkan ƙananan hukumomi 34 da kuma wuraren aiwatar da ayyukan inganta muhalli guda 6,652 a faɗin jihar.
Gwamna Raɗɗa ya ce: “Burinmu a bayyane yake: bishiyoyi miliyan 11 kafin shekarar 2030, inda za mu fara da bishiyoyi miliyan biyu a shekarar 2026. Saƙonmu a taƙaice shi ne: Mutum ɗaya, bishiya ɗaya,”Dikko ya ce.
Ya jaddada cewa za a auna nasarar shirin ne ta yawan bishiyoyin da suka rayu suka girma, ba wai ta yawan tsirran bishiyoyin da aka rarraba wa jama’a ba.
Dikko ya ƙara da cewa: “Tsiron bishiya da aka rarraba wata dama ce, amma bishiyar da ta rayu ta girma nasara ce. Ba za mu ƙirga yawan bukukuwa ba, za mu ƙirga bishiyoyin da suke raye.”
Gwamnan ya bayyana cewa kare muhalli yana da matuƙar muhimmanci ga haɓaka aikin noma, tabbatar da wadatar abinci da kuma samun ci gaba mai ɗorewa. Ya yi gargaɗin cewa kwararowar hamada, sauyin yanayi da ambaliyar ruwa suna barazana ga hanyoyin samun abin rayuwar al’umma da zaman lafiyar yankunansu.
Ya ce: “Haɗarin sauyin yanayi matsala ce da ke da alaƙa da talauci. Yana haifar da hauhawar farashin abinci, ya bar rumbunan hatsi babu komai, ya haddasa rikici kan filaye da ruwa, sannan ya tilasta wa matasa barin ƙauyukansu.”
Raɗɗa ya bayyana cewa bishiyoyi suna kare gonaki daga zaizayar ƙasa da iska ke haddasawa, suna inganta yalwar sinadaran da ke cikin ƙasa, suna samar da ’ya’yan itatuwa da abincin dabbobi, tare da samar da ƙarin hanyoyin samun kuɗin shiga ga al’ummomin karkara.
Ya yi tsokaci kan matakan da jihar ta ɗauka wajen inganta tsarin kula da sauyin yanayi, ciki har da samar da manufar sauyin yanayi ta Jiha, kafa majalisar sauyin yanayi ta Jiha da kuma bibiyar yadda ake kashe kuɗaɗen da aka ware wa ayyukan sauyin yanayi a ma’aikatu, hukumomi da ƙananan hukumomi.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa Katsina ce ta zo ta farko cikin jihohin Najeriya 36 a jerin jihohin da suka fi samun nasara wajen gudanar da ayyukan kula da sauyin yanayi a matakin jihohi na shekarar 2025. Haka kuma, ƙungiyar masu aikin gandun daji ta Najeriya ta yaba da ƙoƙarin jihar wajen inganta tsarin kula da muhalli.
Ya ƙara da bayyana ayyukan da ake gudanarwa ƙarƙashin shirin ACRESAL, tare da haɗin gwiwar bankin duniya da gwamnatin tarayya, ciki har da ayyukan magudanan ruwa a cikin birnin Katsina da ayyukan kare gaɓar kogi a Jibia.
