
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Litinin, 19 ga Oktoba, 2026 Mai Shari’a Sylvanus Oriji na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya yi watsi da ƙarar iƙirarin tauye ‘yanci na Naira miliyan 120 da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya shigar akan Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS da wasu uku.
A yayin hukunci kan shari’ar, Alƙali Oriji ya yi watsi da ƙarar bisa rashin nagarta da hujja, wadda mai ƙarar ya gabatar mata. Haka kuma, mai shari’ar ya umarci a biya kowane ɗaya daga cikin waɗanda aka shigar acikin ƙarar N200,000 a matsayin diyya, waɗanda tsohon gwamnan ne zai biya, wato jimillar N800,000 kenan ga ɓangarori hudun.
A bayanin da aka yi, kotun ta ce wasiƙun gayyata da hukumomin gwamnatin tarayya biyu suka fitar da ke umartar El-Rufa’i ya je gaban kwamitin bincike kan zarge-zargen ake masa, sun cika sharuɗɗan doka kuma ba su tauye masa haƙƙin ba da dokar ƙasa ta ba shi ta wace hanya.
Musamman, alƙalin ya ce Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ba su tauye ‘yancin wanda ya shigar da ƙarar ba ta hanyar gayyatar sa domin ya bayar da ba’asi kan zarge-zargen.
A game da ko an tauye haƙƙin tsohon gwamnan a lokacin da jami’an DSS suka yi yunƙurin kama shi a filin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, kotun ta ce hukumar tana da dama a dokance ta ɗauki matakin doka akan waɗanda ake nema da kama su ko da babu izinin kamu kamar yadda dokokin ‘yan sanda, SSS da NSA suka nuna. Sannan dokokin sun bayar da cikakken ikon karɓe masa fasfo da ya bayyana a matsayin tauye ‘yanci.
