
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ƙoƙarinta na daƙile ayyukan garkuwa da wasu miyagun laifuka acikin al’umma, Rundunar ‘Yan sanda a Jihar Benuwai, ta ce ta yi nasarar ceto wasu mutane guda takwas da aka sace a jihar tare da kama mutum biyu da ake zargi a Ƙaramar Hukumar Ohimini.
Wannan ya biyo bayan al’amarin garkuwa da ya auku a ranar 13 ga Oktoba, 2026 da misalin ƙarfe 10:15 na dare, a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da wani fada na coci da wasu mutane da dama da suke kan hanyar koma wa gidajensu daga wata kasuwar ƙauye akan hanyar Ugbokolo zuwa Ajegbe zuwa Awume, kafin a kai ƙauyen Ipiga na Ohimini.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Orchia Aondongu ne ya bayyana haka a ranar Litinin cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce a yayin da suka samu rahoton, an tura jami’an ‘yan sanda da na mobail tare da wasu jami’an tsaron fararen hula na Jihar Benuwai zuwa yankin domin gudanar da aikin bincike da ceto.
A sanadiyyar haka ne suka yi nasarar ceto mutum takwas. An ceto biyu a ranar 16 ga Oktoba yayin da aka ceto sauran shidan a ranar 18 ga Oktoba. A cewar rundunar, an garzaya da su zuwa Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke yankin Otukpo domin ba su kulawar magani.
Haka kuma, a lokacin da jami’an suke ƙoƙarin ceto mutanen, sun kuma yi nasarar cika hannu da wasu mutum biyu – Echefu Emmanuel da Obonyilor Emmanuel bisa zargin su da hannu a garkuwar. A halin yanzu waɗanda aka kaman suna taimaka wa jami’an a aikinsu na bincike domin kamo sauran ‘yan bindigar da suka tsere tare da tabbatar da gurfanar da dukkan wanda aka samu da hannu a ciki domin su fuskanci hukuncin doka.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Cletus Nwadiogbu, ya bayyana godiyarsa ga Sufeto-Janar na Rundunar IGP Olatunji Disu, Mataimakin Sufeto-Janar (AIGP) ‘yan sandan mobai (PMF) da sauran jami’an tsaro bisa goyon bayansu ga rundunar wajen yaƙi da miyagun laifuka a jihar, yana mai kira ga al’umma da su cigaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai don tabbatar da samun tsaro mai ɗorewa a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.
