
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Dakatattun ‘yan majalisar dokokin Jihar Zamfara guda takwas da a kwanan nan suka fice daga jam’iyyar APC, sun gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda suka jaddada masa biyayyarsu ga jam’iyyar mai mulki. Ƙaramin Ministan Tsaro, jigon jam’iyyar kuma tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ne ya jagorance su zuwa Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
A wata sanarwa da mai taimaka wa Matawalle kan harkokin yaɗa labarai, Ahmad Ɗan-Wudil ya fitar, ya ce ‘yan majalisar sun jaddada cikakken goyon bayansu ga Shugaba Bola Tinubu da kuma matsayarsu ta cigaba da zama a jam’iyyar APC. A cewar sanarwar, Matawalle ya ci alwashin sanya ‘yan majalisar cikin tafiyar Tinubu Again Movement (TAM) domin su yi aiki tare ga Shugaban da ‘yan takarar APC gabanin babban zaɓen 2027.
Waɗannan ‘yan majalisa dai sune kamar haka: Aliyu Ango Kagara (Talata Mafara ta Kudu), Ibrahim Tukur Bakura (Bakura), Faruk Musa Dosara (Maradun ta I), Bashir Abubakar Masama (Bukkuyum ta Arewa), Muktaru Nasiru Kaura (Kaura ta Arewa), Nasiru Abdullahi (Maru ra Arewa), Bashar Bello (Bunguɗu ta Yamma), da kuma Bashar Aliyu (Gummi ta I).
A ranar 26 ga Fabarairu ne aka dakatar da ‘yan majalisar bisa zargin su da ayyukan rashin ɗa’ar aiki, ƙulla makirci da shirya wani zama ba bisa doka ba. Kakakin Majalisar Dokokin jihar, Hon. Bilyaminu Isma’il Moriki ya ce dakatarwar ya gabaci matakin siyasarsu da kuma batun ladabtarwa a zauren majalisar. A wasiƙunsu na yin murabus daga jam’iyyar sun kafa hujja da rashin adalci da rashin haɗin kai acikin masu ruwa da tsakin APC a jihar da kuma yadda ake gudanar da lamarin rashin tsaro a matsayin dalilin barinsu jam’iyyar.
Wani jigon APC mai suna Sani Shinkafi ya bayyana cewa, biyar daga cikin ‘yan majalisar an zaɓe su ne a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar PDP a zaɓen 2023 kana suka koma APC, yayin da uku kuma suka yi nasaraa ƙarƙashin APC. Sannan, ya yi watsi da iƙirarin da ke alaƙanta su da Sanata Abdulaziz Yari, yana mai bayyana rahotannin a matsayin ƙirƙira da aka ɗauki nauyin yaɗawa.
