2027: Yahaya Bello ya bayyana ƙwarin-gwiwar gagarumar nasara akan Natasha

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya bayyana ƙwarin-gwiwarsa ta samun ruwan ƙuri’u da gagarumar nasara zaɓen mazaɓar Kogi ta Tsakiya a babban zaɓen 2027 da ke tafe.

Yahaya Bello ya yi wannan ishara ne yayin wata hira da gidan talabijin na TVC a ranar Lahadi, a lokacin da yake bayyana ƙwarin-gwiwar damarmakin samun nasara gabanin zaɓen, wanda za a yi watan Junairun 2027.

Da aka tambaye shi ko zai iya doke Sanata Natasha Akpotu-Uduaghan mai ci a yanzu, wadda mai tambayar ya bayyana a matsayin fitacciyar ‘yar hamayya, tsohon gwamnan ya ce zaɓen ne zai bayyana matsayinsa a siyasa. “Sakamakon zai yi magana ga kansa,” inji shi.

Ya bayyana cewa, yana fatan samun nasara a karan kansa da kuma ga jam’iyyar APC. “Ruwan ƙuri’u. Gagarumar nasara”, inji Bello.

Yahaya Bello, wanda shi ne gwamnan Jihar kogi daga shekarar 2016 zuwa 2024, yana fatan koma wa kujerar zaɓe ta hanyar wakiltar mazaɓar Kogi ta Tsakiya a zaɓen na 2027.

By Babaji

Leave a Reply