Mace ta haifi ’yan biyar mata cikin mintuna huɗu

Spread the love

Wata mata ’yar ƙasar Nijar ta haifi ’yan mata guda biyar a lokaci guda a wani asibiti mai zaman kansa da ke birnin Cotonou na ƙasar Benin, inda aka haifi yaran cikin minti huɗu kacal.

Lamarin ya faru ne a ranar Talata, 6 ga Oktoba, 2026, a wani asibiti da ke gunduma ta biyar a Cotonou. Rahotanni sun ce an haifi jaririyar farko da misalin ƙarfe 10:43 na safe, yayin da aka haifi ta biyar da ƙarfe 10:47, abin da ya sa aka kammala haihuwar yaran biyar cikin ɗan ƙanƙanin lokaci.

Ma’aikatan lafiya sun tabbatar da cewa haihuwar ta gudana lafiya, kuma mahaifiyar da jariran suna cikin ƙoshin lafiya bayan haihuwar.

Sai dai, saboda yanayin haihuwar da kuma kasancewar yaran ƙanana, an kai su sashen kula da jarirai na musamman domin ci gaba da sa ido kan lafiyarsu.

Rahoton da gidan rediyon Bip Radio ya fitar, wanda wasu kafafen yaɗa labarai suka wallafa, ya nuna cewa an haifi jariran ne bayan cikar watanni takwas na cikin. Ma’aikatan lafiya sun ce babu ɗaya daga cikin jariran da ya buƙaci a ba shi iskar oɗygen a lokacin da aka bayar da rahoton.

Wata likitar lafiya, Pascaline Cakpo Tchi Tchi, ta bayyana cewa mahaifiyar ta daɗe tana fatan samun haihuwa, kuma ta bi wata hanyar magani da ake amfani da ita wajen taimaka wa mace ta samu juna biyu.

A cewarta, gwaje-gwajen da aka yi a lokacin cikin sun nuna cewa matar na ɗauke da ’ya’ya biyar, don haka ta san tun watanni da dama cewa za ta iya haihuwar yara da dama a lokaci guda.

Haihuwa irin wannan ba kasafai take faruwa ba, domin ɗaukar jarirai biyar a cikin mahaifa da kuma haihuwarsu a lokaci guda na buƙatar kulawa ta musamman daga likitoci.

Likitar ta kuma jaddada cewa iyayen jariran za su buƙaci taimako wajen kula da ’ya’yansu biyar, musamman ta fuskar buƙatun yau da kullum da kuma kulawar lafiya da yara ƙanana ke buƙata.

Haihuwar ta sake jawo hankali kan irin nauyin da iyalai ke fuskanta idan aka haifi yara da dama a lokaci guda, musamman a lokacin da suke buƙatar kulawa ta musamman.

By ukarofi

Leave a Reply