An maka bankin FCMB a kotu kan zargin yaɗa bayanan asusun kwastoma ta WhatsApp

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kamfanin First Tirad Global Resources Ltd da babbar mai hannun jarinsa, Funmilola Soyebo, sun shigar da ƙara a kan bankin First City Monument Bank (FCMB), inda suke neman diyyar Naira biliyan 5 bisa zargin fitar da bayanan asusun bankin kamfanin ga wani mutum ba tare da izini ba.

Masu ƙarar, wato kamfanin First Tirad da Soyebo, wadda ita ce mafi yawan mai hannun jari a kamfanin kuma kaɗai aka amince ta sanya hannu kan asusun bankinsa, sun ce suna neman diyyar ne bisa zargin karya sirrin abokan hulɗa, sakaci da kuma tauye haƙƙin sirri.

An shigar da ƙarar ne a Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya (FCT) da ke Abuja, inda masu ƙarar ke zargin bankin da karya wajibcin kiyaye sirrin bayanan kwastomomi, tare da fallasa muhimman bayanan kuɗi, kasuwanci da na mutum. ƙarar mai lamba FCT/HC/NY/255/2026 tana ƙunshe ne a cikin takardar sammaci, bayanin ƙarar da kuma shaidar da aka rantsar, waɗanda lauyoyin masu ƙarar, Oluchi ɓiɓian Uche, Okueyelegbe Sylɓanus Maliki da sauran lauyoyi suka shigar.

A cikin bayanin ƙarar, First Tirad ya ce yana da asusun kamfani a FCMB, inda aka ware Soyebo a matsayin mutum ɗaya tilo da aka ba izinin sanya hannu kan asusun. Masu ƙarar sun yi zargin cewa bankin ya bai wa wani mutum na daban bayanan asusun kamfanin, duk da cewa mutumin ba shi da izini ko wata takardar wakilci da za ta ba shi damar samun bayanan kuɗin. Sun ce an fitar da bayanan ne ba tare da saninsu, amincewarsu ko izininsu ba, kuma hakan ya saɓa wa ƙa’idojin da bankin ya tanada domin kare sirrin bayanan kwastomominsa.

A cewar masu ƙarar, lamarin ya faru ne a ranar 8 ga Afrilu, 2026, lokacin da wani mutum ya tuntuɓi tsohon jami’in kula da asusun FCMB, Taofeeƙ Are, ta manhajar WhatsApp, yana neman bayanan asusun kamfanin na tsakanin 1 ga Janairu zuwa 8 ga Afrilu, 2026. Sun yi zargin cewa daga nan Are ya tuntuɓi wani jami’in bankin da ke aiki a lokacin, Olutunde Oyasola, wanda ya samar da bayanan asusun tare da aika masa hotunan allo na bayanan.

Masu ƙarar sun ƙara da cewa daga bisani an tura waɗannan hotunan ga mutumin da ya nemi bayanan ta WhatsApp. Sun ce wannan aika bayanai ba ta da izini, kuma ta saɓa wa wajibcin da ke kan bankin na kare bayanan kuɗi da na kasuwanci na kwastomominsa.

Haka kuma, sun yi zargin cewa bayanan asusun sun ƙunshi wasu bayanai masu muhimmanci, ciki har da bayanan biyan kuɗin haya da suka bayyana adireshin gidan Soyebo da sauran bayananta na sirri. A cewarsu, fallasa bayanan ya karya sirrin bayanan kuɗin kamfanin tare da jefa bayanan sirri na Soyebo cikin haɗari.

By ukarofi

Leave a Reply