NDLEA ta kama tsohuwa ’yar shekara 83 kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi

Spread the love

Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) ta sake kama wata tsohuwa mai shekaru 83, mai suna Uloma Uchechi Sunday, bisa zargin komawa harkar safarar miyagun ƙwayoyi bayan an taɓa kama ta kuma aka yanke mata hukunci kan irin wannan laifi.

An kama tsohuwar ne a ranar Laraba, 7 ga Oktoba, 2026, a gidanta da ke yankin Ite-Uzo, Umuaguma, ƙaramar hukumar Obingwa ta Jihar Abia.

Kakakin hukumar NDLEA mai kula da yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Femi Babafemi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

A cewar hukumar, sake kama tsohuwar ya biyo bayan samun bayanan sirri da suka nuna cewa tana gudanar da wani wurin da ake zargin ana safarar miyagun ƙwayoyi, wanda kuma ake zargin yana zama mafakar wasu mutane da ke tayar da hankali a yankin.

Hukumar ta ce, jami’anta sun gudanar da aikin ne bayan samun bayanan sirri, inda aka kama tsohuwar a gidanta.

Wani rahoto ya nuna cewa jami’an sun gano wasu miyagun ƙwayoyi da suka haɗa da methamphetamine da kuma wani nau’in ƙwayar maye da ake kira Colorado, waɗanda ake zargin an ɓoye a jikinta ta hanyar ɗaure su a ƙugu da wani zani.

By ukarofi

Leave a Reply