
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wani ma’aikaci ya samu wasu ƙananan raunuka a lokacin da wani gini mai tsawon hawa biyar ya ruguje a layin Durban Street da ke unguwar Wuse II a Abuja, kamar yadda Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta bayyana.
Wannan al’amari ƙari ne akan yawan aukuwar rushewar gine-gine da ake fuskanta a Babban Birnin Tarayya (FCT) a ‘yan watannin nan, ciki har da ruftawar wani gida mai tsawon hawa uku a unguwar Wuse Zone 4 a watan Satumba da wani a yankin Durumi 3 a watan Mayu, wanda ya yi ajalin mutum biyar.
NEMA ta ce, ofishinta na Abuja ya samu labarin aukuwar lamarin na Wuse II ne a ranar Asabar, 17 ga Oktoba, 2026 da misalin ƙarfe 6:30 na yamma, lamarin da ya sa ya hanzarta tura jami’an hukumomi masu ruwa da tsaki domin gudanar da aikin kwana-kwana.
A wata sanarwa da sashen yaɗa labaranta ya fitar, hukumar ta ce ofishin hukumar kashe gobara na FCT yana daga cikin hukumomin da suka tura jami’ai yayin da tawagarsa na bayar da agajin gaggawa da ke yankin AYA ya garzaya gurin domin gudanar da aikin bincike da ceto. Ta bayyana cewa, babu wani rai da aka rasa a sanadiyyar faruwar al’amarin kuma ta tabbatar da cewa an garzaya da ma’aikacin da ya jikkata zuwa wani asibiti mafi kusa da wajen da abin ya faru domin ba shi kulawa.
Manhaja ta ruwaito cewa, a watan Satumba ne dai wani gini mai tsawon hawa uku a Wuse Zone 4 ya rushe sa’o’i bayan sashen kula da lamuran ci-gaban Hukumar Raya Birnin Tarayya (FCTA) ta rufe shi da umartar mutanen da suke ciki su fice. ‘Yan sanda sun ce bincike ya nuna cewa da fari an yi wa ginin alama kuma an rufe shi yayin da aka kuma ƙaddamar da atisayen ceto.
Wani labarin, an ceto mutane biyu a wani gida mai tsawon hawa guda da ya ƙunshi ciki da falo guda shida a yankin Kubwa 2/2. Al’amarin ya auku ne a Agusta, kuma a lokacin ne aka garzaya da mutanen zuwa Babban Asibitin Kubwa a matsakaicin hali.
Sannan, a watan Mayu ne wani gini mai tsawon hawa uku da ake aikin ƙararsa ginawa ya rufta a unguwar Durumi 3, kusa da kasuwar Gudu, inda ya yi ajalin mutum biyar. An yi nasarar ceto mutane 15 da suka maƙale acikin buraguzan gini, inda aka samu tara a raye da wani guda a mawuyacin hali.
Akan haka ne Ministan Abuja, Nyesom Wike ya umarci a gudanar da cikakken bincike tare da gargaɗin ‘yan kwangila da masu bayarwa da su kula da tare da bada cikakken haɗin kai ga sharuɗɗan gini da kuma ƙyale jami’an gwamnati su riƙa zuwa ziyarar sanya ido yayin da ake gudanar da ayyukan gine-gine.
