Rev Kuje ya yi kira ga Kiristoci su rayu cikin hasken Allah

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

An yi kira na musamman ga kiristoci da su rayu cikin hasken Allah tare da guje wa ayyukan duhu domin su samu shiriya da albarkar Ubangiji.

Kiran ya fito ne daga bakin Rabaran mai kula da cocin ECWA Ombi 2 da ke Lafia jihar Nasarawa wato Rabaran Innocent A. Kuje a yau Lahadi yayin wa’azinsa na ranar Lahadi kan taken, “Rayuwa Cikin Hasken Allah.”

Mai wa’azin yace duk wanda ya bar haskenshi a kunne shi ne yake tafiya tare da Allah yana mai cewa irin wannan mutum baya barin komai na duniya ya ɗauke masa hankali.

“Don barin haskenka a kunne dole ne ka kuɓuta daga zunubanka. Idan da duk duniya na da wannan haske to duk wasu miyagun abubuwa ba za su faru ba,” in ji shi.

Ya bayyana cewa dole ne Kiristoci su yi hadaya don cigaba da haskaka haskensu, yana mai jaddada buƙatar su amince cewa masu zunubi ne kuma su nemi tuba na gaskiya.

“Mutane ba sa rayuwa cikin hasken Allah suna yin yadda suka ga dama. A matsayinmu na Kiristoci ya kamata mu ɗauki wannan haske zuwa ga waɗanda ba su ba da gaskiya ba,” in ji shi.

Da yake kawo nassi daga Littafin Afisawa Sura ta 5 aya ta 8 zuwa ta 14, malamin yace nauyi ne da ya rataya a wuyan Kiristoci su fallasa ayyukan shaiɗan tare da yaɗa hasken Allah ga masu zunubi.

“Dole ne mu miƙa wannan haske zuwa gare su, ba za su iya yin wani abu mai kyau ba saboda sun rasa haske. Mu jarraba kanmu don ganin ko hasken na haskakawa. Wani lokacin mun yi imani da hasken amma ba ma yaɗa shi ga wasu,” in ji shi.

Ya kuma yi kira ga muminai Kiristocin jihar da duniya baki ɗaya su guji ƙarya maimakon haka su yi rayuwa cikin tsarki a kowane lokaci da kuma duk inda suka tsinci kansu, yana mai bayyana cewa haske yana wakiltar Allah.

A cewarsa, fa’idojin tafiya cikin haske sun haɗa da samun albarka a dukkanin lamura, samun shiriya da haske daga Allah, kyakkyawar alaƙa da Allah, kwanciyar hankali, kariya da kuma ‘yanci kamar yadda manzannin Kiristi suka koyar a littafi mai tsarki.

Wakilinmu ya kuma ruwaito cewa hidimar ranar Lahadin ta kuma haɗa da waƙoƙin yabo daga ƙungiyoyin mawaƙa daban-daban na cocin tare da addu’o’i na musamman da ayyukan annabta da sauransu.

By ukarofi

Leave a Reply