Daga JOHN D. WADA a Lafia
An samu tashin hankali a garin Ome, yankin rayawa na Jenkwe da ke ƙaramar hukumar Obi a Jihar Nasarawa a jiya Lahadi da yamma, bayan kisan gillar da aka yi wa wani jami’in hukumar tsaron daji ta Najeriya wato Nigerian Forest Security Service (NFSS) a turance maisuna Mista Lawrence Cletus, mai shekaru 39.
Ana zargin Fulani makiyaya ne suka aikata ɗanyen aikin a lokacin da mamacin yake ƙoƙarin hana su lalata gonakin manoma a yankin.
Jaridar Manhaja ta tattara cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6:30 na yamma kusa da bakin kogi a cikin al’umma, bayan da aka kai ƙorafin mamaye gona a ofishin ‘yan sanda na Ome domin neman ɗauki.
A cewar majiyoyi da suka zanta da wakilin mu, jami’in tsaron dajin ya gamu da ajalinsa ne jim kaɗan bayan jami’an NFSS sun kama wasu mutane kan mamayewar. An ce maharan sun kai masa hari, suka kashe shi tare da jefa gawarsa a cikin kogin.
Wata shaida da ba ta so a bayyana sunanta ta ba da labarin yadda makiyayan suƙa riƙa bin mamacin da gudu kafin su kashe shi har lahira.
A cewar shaidar, “Na ga makiyaya suna rige-rigen kashe shi har na dinga ihu ina gaya wa mamacin ya ƙara gudu domin tsira da ransa lokacin da na ga suna rige-rigen kashe shi.”
Tace mazauna garin sun garzaya zuwa wurin bayan sun ji labarin kisan kuma sun ciro gawarsa daga cikin kogin.
Da wakilin mu ya tuntube shi don jin ta bakinsa game da mummunar lamarin jami’in ‘yan sanda da ke kula da yankin (DCO) da aka tura zuwa yankin wato Habib Isa, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa ya kai rahoton batun zuwa hedikwatar ‘yan sanda ta shiyya kuma an fara bincike domin cafke waɗanda suka aikata laifin.
Ya buƙaci al’umma da su cigaba da zama lafiya kuma su cigaba da gudanar da harkokin nomansu na yau da kullum tare da tabbatar musu da cewa jami’an tsaro za su shawo kan lamarin.
A martaninsa, dagacin garin Ome, Mista Luka Zhemuga, ya yi Allah wadai da kisan, yana mai bayyana shi a matsayin abin takaici kuma mara amfani.
Yayin da yake kira ga mazauna garin da su cigaba da bin doka da oda, basaraken gargajiyan ya kuma bayyana cewa a yanzu haka an sanar da hukumomin da abin ya shafa kuma ana ƙoƙarin bankaɗo waɗanda suka aikata laifin domin su zama izina ga wasu.
Binciken Manhaja ya gano cewa marigayi Lawrence Cletus da aka halaka ya mutu ya bar mata biyu da yara biyar a duniya.
