
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar Sojin Saman Nijeriya NAF, ta yi nasarar halaka wasu jiga-jigan mayaƙan ƙungiyar Islamic State West Africa Province (ISWAP) a yankin Tafkin Chadi sakamakon wani harin sama na luguden wuta da ta yi a maɓoyarsu.
Kakakin NAF, Air Komodo Ehimen Ejodame ne ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar a jiya Talata, inda ya bayyana al’amarin a matsayin gagarumar nasarar akan ‘yan ta’adda a yankin Tafkin Chadi bayan wani hari ta sama da jami’an rundunar suka ƙaddamar a maɓoyar mayaƙan a ranar 19 ga Oktoba, 2026.
Wani bincike da aka gudanar bayan ƙaddamar da farmakin ya nuna cewa an halaka mayaƙan ISWAP da dama ciki har da wasu fitattu da ke cikin kwamitin jagorancin ƙungiyar kamar su Jindullah, wanda shi ne shugaban tsaro da Abu Saleem da aka sani da Abul Kissa, wanda mamba ne na majalisar shura ta ISWAP.
Harin dakarun tsaron ya kuma lalata kayan aikin ‘yan ta’addar ciki har da injinan jiragen ruwa da baburan da mayaƙan suke amfani da su wajen zirga-zirgar ayyukansu, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Ejodame ya bayyana cewa, wannan wani ɓangare ne na ƙoƙarin NAF wajen lalata hanyoyin aikata miyagun laifuka da bunƙasa lamuran tsaro a Arewa maso Gabas. Wannan hari ya haifar da gagarumar faɗuwa ga ƙungiyar ISWAP da ayyukanta na shirya hare-hare da ƙaddamar da farmaki akan ƙauyukan da fararen hula suke zama.
Tuni dai Babban Hafsan Rundunar, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke ya jaddada aniyar NAF ta cigaba da ƙaddamar da hare-hare akan sansanonin ‘yan ta’adda a ƙoƙarinsu na dawo da zaman lafiya da ɗorewar al’amura a shiyyar Arewa maso gabashin Nijeriya da sauran sassan ƙasar baki ɗaya.
