Trump ya fara take-taken ƙwace wa ’yar majalisa, Ilhan Omar takardar zama ’yar Amurka

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ta fara binciken da ka iya kaiwa ga ƙwace wa ’yar Majalisar Dokokin ƙasar, Ilhan Omar, takardar zama ’yar ƙasa, sannan a kori ta daga ƙasar, a cewar wani rahoto da jaridar The Wall Street Journal ta wallafa, bisa bayanan jami’an Amurka da wasu mutanen da ke da masaniya kan binciken.

Jaridar ta ruwaito a ranar Laraba cewa binciken ya ta’allaka ne, a wani ɓangare, kan yadda wakiliyar majalisar dokokin Amurka mai wakiltar jihar Minnesota ta samu zama ’yar ƙasar bayan ta isa Amurka a matsayin ’yar gudun hijira daga Somaliya. Rahoton ya ce, hukumomin Amurka na nazarin bayanan shige da fice na iyalinta, kuma sun aika da sammacin kotu fiye da 12, ciki har da ga wasu ’yan uwanta, domin su bayar da shaida a gaban babban alƙali mai sauraron shari’o’in manyan laifuffuka a Minnesota.

Sai dai ofishin Ilhan Omar ya yi watsi da binciken, yana mai bayyana shi a matsayin wanda ba shi da tushe, kamar yadda ya shaida wa jaridar. Rahoton na The Wall Street Journal ya fito ne kwanaki kaɗan bayan jami’an gwamnatin tarayya ta Amurka sun kai samame gidan Omar.  Ofishinta ya bayyana matakin a matsayin wani sabon salo mai tsanani da ba a taɓa ganin irinsa ba, na gwamnatin Trump wajen matsa wa abokan hamayyarta na siyasa.

An kai samamen ne makonni kaɗan kafin zaɓen tsakiyar wa’adin majalisar dokokin Amurka, wanda za a gudanar a ranar 3 ga Nuwamba. Zaɓen na da matuƙar muhimmanci ga jam’iyyar Republican, wadda ke ƙoƙarin riƙe rinjayenta a Majalisa. Omar na neman sake lashe zaɓe karo na biyar domin ci gaba da wakiltar gundumar zaɓe ta biyar ta jihar Minnesota a Majalisar Wakilan Amurka.

Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida ta Amurka ta ce an gudanar da samamen ne a matsayin wani ɓangare na binciken da hukumomin tarayya ke ci gaba da yi. A cewar mutanen da ke da masaniya kan samamen, jami’an tsaro sun ƙwace fasfo ɗin Omar, wayarta ta hannu, kwamfutocinta na sirri da kuma wasu littattafan rubutu. Omar ta isa Amurka a shekarar 1995, bayan ta zauna a sansanin ’yan gudun hijira a Kenya. Daga bisani, ta samu zama ’yar ƙasar Amurka a shekarar 2000. A baya, ta sha musanta aikata zamba a harkokin shige da fice.

Jaridar ta ce ɗaya daga cikin batutuwan da ake bincike a kai shi ne ko Omar ko mahaifinta marigayi sun sauya shekarunta a cikin takardun shige da fice, domin nuna cewa tana da shekara 17 maimakon 18 a lokacin da mahaifinta ya nemi zama ɗan ƙasar Amurka. A cewar rahoton, masu bincike na duba ko wannan sauyin shekarun ya taimaka wajen ba Omar damar samun zama ’yar ƙasa ta hanyar mahaifinta, maimakon ta bi wata hanya ta musamman domin neman takardar zama ’yar ƙasa da kanta.

Mahaifin Omar ya rasu a shekarar 2020, lamarin da ya ƙara wahalar tattara hujjojin da za su tabbatar ko Omar ta yi ƙarya game da shekarunta, ko kuma mahaifinta ne ya bayar da bayanan ƙarya a madadinta. Jaridar ta ruwaito cewa, a cewar wani tsohon babban jami’in shige da fice a Ma’aikatar Shari’a ta Amurka, gwamnatin Trump za ta dogara ne kan irin waɗannan hujjoji wajen gina hujjar da za ta iya amfani da ita a kan Omar.

Rahoton ya kuma bayyana cewa jami’an sashen binciken tsaron cikin gida na Amurka sun taɓa bincikar irin wannan zargi a lokacin gwamnatin tsohon Shugaban ƙasa Joe Biden, amma ba su ci gaba da ɗaukar mataki ba saboda rashin isassun hujjojin da za su tabbatar da zamba. Sai dai jaridar ba ta ce an shigar da ƙara a kotu domin neman soke zama ’yar ƙasar Omar ba. Irin wannan mataki zai buƙaci a bi tsarin shari’a, domin bincike kaɗai ba ya soke zama ɗan ƙasa ko kuma ba da izinin korar mutum daga ƙasar.

Rahoton ya kuma ce wata hukumar sa ido ta Majalisar Dokokin Amurka mai zaman kanta daga jam’iyyu ta taɓa wanke Ilhan Omar daga zargin aikata ba daidai ba dangane da bayanan kadarorinta, waɗanda aka ce sun nuna ƙimar dukiyarta fiye da ainihin abin da take da shi. Jami’an Sashen Binciken Tsaron Cikin Gida (HSI), wanda ke ƙarƙashin Hukumar Shige da Fice da Kwastom ta Amurka (ICE), sun gudanar da binciken gidan Omar bisa sammacin bincike da kotu ta amince da shi, a cewar Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida.

A safiyar ranar Litinin, jami’an tsaro sun toshe hanyar da ke kewaye da gidan Omar, sannan suka fitar da wasu kwalaye masu ɗauke da takardun da ke nuna cewa kayayyakin da ke cikinsu hujjoji ne da aka ƙwace yayin bincike. Ilhan Omar, wadda fitacciyar ’yar siyasa ce a ɓangaren masu ra’ayin kawo sauye-sauye a jam’iyyar Democrat, ta shafe shekaru tana fuskantar hare-haren suka daga Trump da magoya bayansa saboda asalinta na Somaliya da kuma tarihin shigarta Amurka.

Sa’o’i kaɗan bayan samamen da aka kai gidanta ranar Litinin, Trump ya shaida wa manema labarai cewa ba shi da alaƙa da aikin, yana mai cewa batun yana ƙarƙashin ikon Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ne.

By ukarofi

Leave a Reply