An umarci ƙananan hukumomin Katsina su gabatar da ayyukan da aka kammala ba a biya ba

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Mai ba gwamnan Katsina shawara kan ayyukan ƙananan hukumomi, Hon. Lawal Rufa’i Safana, ya umurci kowacce ƙaramar hukuma ta gabatar cikin kwanaki bakwai da jerin ayyukan da aka kammala amma ba a biya kuɗinsu ba, ta hannun Resident Inspector (R.I.) na kowace ƙaramar hukuma.

Umarnin ya fito ne a yayin ƙaddamar da zaman nazarin kasafin kuɗin ƙananan hukumomi na shekarar 2027.

A jawabin nasa, Hon. Safana ya jaddada muhimmancin tattara bayanai sahihai kan ayyukan da aka kammala ba tare da biyan kuɗinsu ba, domin samun cikakken bayani da zai taimaka wajen tantance halin da ake ciki da ɗaukar matakan da suka dace.

Ya buƙaci ƙananan hukumomi su tabbatar da cewa jerin ayyukan da za su gabatar sun bi ta hannun Resident Inspectors (R.I.) domin tantancewa da tabbatar da sahihancinsa.

Shirin na daga cikin matakan da gwamnati ke ɗauka domin tabbatar da inganci da sahihancin kasafin kuɗin ƙananan hukumomi na shekarar 2027, kafin gabatar da shi da kare shi a gaban kwamitin kula da ƙananan hukumomi na majalisar dokoki ta Jihar Katsina.

Zaman ya samu halartar babban sakatare na ma’aikatar ƙananan hukumomi da harkokin masarautu ta Jihar Katsina, babban mai hukumomi da daraktocin ma’aikatar.

By ukarofi

Leave a Reply