Da Ɗumi-Ɗumi: Shugaban ƙungiyar Afenifere, Fasoranti ya rasu a shekara 100

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shahararren jagoran ƙungiyar nan ta ƙabilar Yarabawa a siyasa da zamantakewa ta Afenifere, Pa Reuben Famuyide Fasoranti ya rasu, bayan shafe shekaru 100 a duniya.

Gwamnan Jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa ne ya sanar da rasuwar a wata wasiƙar ta’aziyya da ya fitar a ranar Talata, 20 ga Oktoba, 2026, inda ya bayyana marigayin a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙasa kuma abin kwaikwayo bisa hikima, kima da hidimarsa ga ƙasa.

Aiyedatiwa ya bayyana cewa, marigayin ya bayar a gagarumar gudunmawa wajen ci-gaban Jihar Ondo, ƙasar Yarabawa da ma Nijeriya baki ɗaya, yana mai ƙarawa da cewa, za a yi kewar shawarwarinsa a matsayinsa na uba da ƙoƙarin tsayar da gaskiya da adalci da kuma shugabanci na gari acikin al’umma.

Gwamnan a madadin gwamnatin jihar da al’ummarta, ya miƙa saƙonsa na ta’aziyyarsa ga iyalai da dangin Fasoranti, al’ummar Masarautar Akure da baki ɗaya jihar bisa babban rashin. A ƙarshe, ya yi masa addu’ar fatan samun rahamar ubangiji.

By Babaji

Leave a Reply