Gwamnatin Kano ta rufe asibitocin kuɗi 35 kan saɓa wa dokokin aiki

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar kula da Cibiyoyin Lafiya na Kuɗi ta Jihar Kano (PHIMA), ta sanar da rufe wasu asibitocin kuɗi sama da guda 35 a faɗin jihar bisa samun su da hannu a saɓa wa ƙa’idojin gudanarwa na tsawon shekara guda. Darakta-Janar ta PHIMA ta riƙo, Hajiya Khadijah Sa’id ce ta bayyana haka a wata hira da manema labarai daga Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa (NAN) a Kano, ranar Talata.

Hajiya Khadijah, wadda kuma ita ce daraktar gudanarwa da sauran ayyuka, ta ce matakin da aka ɗauka akan cibiyoyin lafiyar ɓangare ne na ƙoƙarin tilasta tsare dokokin gudanarwa da bayar da kariya ga mazauna daga karɓar magani a cibiyoyin lafiya marasa aminci a gare su da hukumar take yi a faɗin jihar.

Ta bayyana aiki ba tare da lasisi ba, rashin sabunta rajistar shekara da ɗaukar waɗanda ba su cancanta ba aiki a matsayin manyan ayyukan karya dokokin da suka gano yayin atisayen da jami’ansu suka gudanar. A cewarta, sun samu sama da asibitoci 100 da suka saɓa wa doka guda ko sama da haka, saidai sun rufe sama da 35 da karya dokokin nasu ya wuce kima da ba za ta iya lamunta ba.

Daraktar riƙo ta bayyana cewa, an rufe wasu asibitocin na wucin-gadi domin bai wa masu su damar gyara kurensu da aka gano kafin a sake buɗe su. Saidai, ta ce dukkan wata cibiya da aka rufe bisa wasu manyan laifuka, za su cigaba da kasancewa a rufe kuma masu su ba su da damar amfani da lasisin aikinsu wajen buɗe wasu cibiyoyin karɓar magani.

Ta ƙara da cewa, hukumar ta ƙarfafa matakan aikin sintiri domin tabbatar kiyaye dokoki da sharuɗɗan mallakar lasisin aikin kiwon lafiya da ƙa’idojin ƙwarewa a sassan ƙananan hukumomi 44 na faɗin jihar.

By Babaji

Leave a Reply