
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da ɓullar cutar Ebola a Babban Birnin Tarayya Abuja, da ya haɗa da wata mata da a kwanan nan ta shigo Nijeriya daga wani jirgin ƙasa-da-ƙasa daga ƙasar Uganda. Ministan Lafiya da Walwalar Al’umma, Farfesa MuhamAli Pate ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 20 ga Oktoba, 2026 biyo bayan wata tabbatarwa kan ɓullar cutar daga ɗakin binciken masana harkar lafiya.
A cewar sanarwar, an kai mara lafiyar ne wani asibitin kuɗi da ke Abuja, inda aka kula da ita na tsawon kwanaki da dama kana wani bincike ya tabbatar da cewa tana ɗauke da cutar. A halin yanzu an keɓance ta kuma tana karɓar magani. Farfesa Pate ya bayyana cewa, an fara bin diddigi, inda aka gano mutane 44 da suke ɗauke da alamun cutar a jikkunansu, yayin da tawagogin lafiya suke aikin ƙoƙarin gano sauran mutanen da cutar ta shafa, ciki har da ma’aikatan lafiya, marasa lafiya, masu aikin raino da masu harkar tafiye-tafiye.
Ya ce, Ma’aikatar Lafiya da Walwalar Al’umma ta Tarayya, Cibiyar kula da bayar da Kariya ga Cutuka ta Ƙasa (NCDC), sakatariyar lafiyar FCT da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki, suna aiki tare domin daƙile cigaba da yaɗuwar cutar acikin al’umma. Ya ƙara da cewa, ana sanya ido kan halin da ake ciki, yayin da ake kuma bayar da tallafin daƙile yaɗuwar cutar ga asibitin da aka kwantar da marasa lafiyar tare da ɗaukar wasu muhimman matakan kariya.
Akan haka ne ministan ya kirayi al’umma da cibiyoyin lafiya masu zaman kansu a faɗin Nijeriya da su kasance a ankare, yana mai shawartar ma’aikatan lafiya da su riƙa kula da zara sun ga wani abin zargi tare da gaggauta ɗaukar matakan lafiyar da suka dace, sannan su hanzarta sanar da hukumomin lafiya na gwamnati.
Kazalika, ya bayyana cewa Ebola tana yaɗuwa ne ta hanyar haɗuwa kai-tsaye da jini ko jikin mara lafiyar da ke ɗauke da ita ko kuma wanda ya rasu a sanadiyyar kamuwa da cutar da kuma haɗuwa da kayayyakin da suka gurɓace, yana mai kira ga al’umma da su gaggauta sanar da jami’an lafiya da zarar sun ga alamun ɓullar cutar yankunansu.

