
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar Liverpool ta ƙulla yarjejeniyar baka da Paris Saint-Germain akan siyan ɗan wasa Bradley Barcola. A yanzu hada-hadar tana matakin ƙarshe bayan samun cimma matsaya a tattaunar ɓangarorin biyu, kamar yadda Fabrizio Romano ya ruwaito.
An ƙulla yarjejeniyar ne akan Yuro miliyan 140, wato kwatankwacin Fam miliyan 120. Ainihin farashin shi ne £100m (€117m) da kuma €22m a matsayin ƙari. Tuni dai Barcola ya amince da koma Liverpool a yarjejeniyar kwantaragi mai tsawo
Liverpool ta fara kwaɗayin siyo ɗan Faransan mai shekaru 23 ne ne tun watan Mayu. Da fari PSG tana neman Yuro 170m, amma daga bisani bayan tsawon makonni ana tattaunawa tsakanin daraktoci, Zakaran Faransan ya rage adadin ya buƙata.
Barcola dai shi ne wanda ya taimaka wa cikar yarjejeniyar bayan shaida wa PSG cewa ba zai tsawaita zamansa da ita ba sama da 2028. Ɗan wasan, wanda ya lashe UEFA Champions League sau biyu, ya buga wasanni 49 a kakar wasan da ta gabata, inda ya zura ƙwallo 13 ya kuma bayar da 7 aka ci.
