Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Ƙungiyar Miyetti Allah reshen ƙaramar hukumar Zuru ta karrama Sanata Musa Garba Maidoki Sanata mai wakiltar gundumar Kebbi ta kudu.
Shugabannin ƙungiyar miyetti Allah na ƙaramar hukumar ta Zuru sun bayyana cewa ɗan majalisar dattijan ya cancanci wannan karramawar bisa irin gagarumin ƙoƙari da jajircewar da ya ke nunawa wajen tallafa wa harkokin tsaro da zaman lafiya a yankin da ya ke wakilta.
An shirya gabatar da wannan karramawa ne jiya yayin bikin taron ƙaddamar da shugabannin yaƙin neman zaɓe na jam’iyyar ADC ne saboda a nuna wa al’ummar jihar Kebbi irin ƙoƙarin da ya ke yi wanda ya sanya mutanen da ya ke wakilta suna tare da shi.
Wannan karramawa shaida ce ta yadda al’umma ke ganin gudunmawar Sanata Maidoki wajen neman mafita ga matsalolin tsaro da kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Haka kuma, abin farin ciki ne ganin ƙungiyoyin al’umma suna gane wa tare da yaba wa waɗanda ke taka rawa wajen tabbatar da zaman lafiya
