Yadda maulidin a zawiyyar Ahlul Faidhati Mai Diwani ya ƙayatar a Kaduna

Spread the love

Daga ZAHRADDIN ILYASU

Zawiyyar Ahlul Faidhati Mai Diwani Group ta gudanar da gagarumin taron Maulidin Manzon Allah (SAW) na watan Rabi’ul-Awwal na shekarar 1448/2026, inda aka shafe tsawon dare har wayewar gari ana gudanar da al’amura daban-daban domin karfafa soyayya ga Manzon Allah (SAW) da ɗabbaƙa koyarwarsa a aikace.

Taron ya ƙunshi karatun Al-Ƙur’ani, zikiri, rera yabo da salati ga Manzon Allah (SAW), da gaisuwar sada zumunci, da mika kyaututtuka da takardun shaidar kammala haddace wasu littattafai, baya ga addu’o’i na musamman da aka gudanar a karshen zaman.

A yayin taron, babban shehin zawiyyar, Shehu Ismaila Umar Almaddah ya gabatar da dogon karatu, inda ya yi bayani kan muhimmancin murna da zagayowar lokacin haihuwar Annabi Muhammadu (SAW) da kuma nuna soyayya gare shi. Ya bayyana cewa watan Rabi’ul-Awwal lokaci ne na murna da zagayowar lokacin haihuwar Manzon Allah (SAW), da kuma tuna babbar ni’imar da Allah Ya yi wa duniya ta hanyar aiko Manzonsa a matsayin rahama ga dukkan halittu.

Shehu Ismaila Umar Almaddah ya kuma yi bayani kan ma’anar soyayya da nau’o’inta, yana mai jaddada cewa soyayya ta gaskiya ga Manzon Allah (SAW) ba ta tsaya kawai ga furuci ba, sai an hada ta da koyi da kyawawan halayensa.

Har ila yau, Shehun ya yi kira ga malamai da masu ilimi da su kara kokari wajen isar da sakon Manzon Allah (SAW) ga dukkan al’umma, ba tare da takaita shi ga wata kabila, yare ko nahiya guda ba, domin Manzon Allah (SAW) ma’aiki ne ga dukkan halitta.

Ya kuma jaddada muhimmancin hada ilimin addini da ilimin zamani, yana mai kira ga al’umma da su dage wajen neman ilimi, samun kwarewa da wayewa domin samun ci gaba. Haka kuma, ya yi kira ga karfafa zaman lafiya da hadin kan al’umma, yana mai cewa abubuwan da suka hafa mutane sun fi wadanda suka raba su yawa.

Taron ya samu halartar wakilan Al-Ummah, inda Shehu Ismaila Umar Almaddah ya yaba musu bisa halartar taron. Wasu daga cikin wakilan sun samu damar gabatar da sakonnin gaisuwa da fatan alheri daga al’ummominsu cikin harsuna daban-daban, ciki har da Turanci, Faransanci, Larabci da Fulatanci, tare da sauran harsuna, domin isar da sakonnin gaisuwa da maraba ga bakin Manzon Allah (SAW).

Kamar yadda aka saba gudanarwa a irin wannan taro dai, an gabatar da karatuttuka daban-daban da suka hada da karatun Alkur’ani da Tahni’a, tare da sauran karance-karance, zikiri, salati da yabo ga Manzon Allah (SAW).

A wani ɓangare na maulidin kuma, an mika takardun shaida ga daliban da suka samu nasarar haddace Diwani baki daya, da wadanda suka haddace Rihilolin Shehu Ibrahim baki daya, da kuma masu haddar Goran Faila.

Haka kuma, Shehu Ismaila Umar Almaddah ya gabatar da zane suna ga jariran da aka haifa, inda ya yi musu addu’ar samun albarka, kyakkyawar rayuwa da makoma mai kyau. Ya kuma yi wa mahalarta taron fatan alheri, tare da addu’ar Allah Ya sa kowa ya koma gidansa cikin farin ciki, kwanciyar hankali da samun babban rabo.

An gudanar da addu’ar karshe da misalin karfe 5:30 na safe, inda aka yi addu’a ga Afirka da duniya baki daya, tare da rokon Allah Ya kawo zaman lafiya, tsaro, arziki da ci gaba ga al’umma. Daga bisani aka gudanar da Sallar Asuba, tare da sauran addu’o’in da ake gudanarwa a karshen taron Maulidin.

Taron ya kasance wata dama ta hada al’umma a kan soyayya ga Manzon Allah (SAW), murnar zagayowar lokacin haihuwarsa da kuma karfafa gwiwar matasa da sauran al’umma wajen neman ilimi, zaman lafiya da hadin kai.

By Babaji

Leave a Reply