Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ta fara wani taron ƙasa da ƙasa na tsawon kwanaki biyu, wanda Sashen Kimiyyar Ƙasa da Muhalli na jami’ar ya shirya, domin tattauna hanyoyin da za a ƙara sanya al’umma cikin ayyukan yaƙi da sauyin yanayi da kuma samar da birane masu ɗorewa da dacewa da rayuwa.
Taron, wanda aka yi shi a sashin kimiyyar Ƙasa na jami’ar wanda shi ne karo na biyu, taken taron na bana shi ne:
“Gina makoma mai juriya: Matsugunan da ba a tsara su ba da matakan yaƙi da sauyin yanayi da al’umma ke jagoranta domin samar da muhalli mai dacewa da rayuwa.”
Da yake buɗe taron, Shugaban Sashen, Farfesa Abdulazeez Raji, ya bayyana cewa sama da mutane biliyan ɗaya ne a faɗin duniya ke rayuwa a unguwannin awon igiya, inda yawancinsu ke fuskantar barazanar sauyin yanayi. Ya ce bai kamata a ɗauki mutanen da ke irin waɗannan wurare a matsayin matsala ba, sai dai a matsayin abokan hulɗa, saboda iliminsu da gogewarsu na iya taimakawa wajen samar da hanyoyin magance matsalolin muhalli.
Farfesa Raji ya ce ƙudirin Najeriya na rage hayaƙi da ke haifar da ɗumamar yanayi da kashi 32 cikin 100 nan da shekarar 2035, da kuma cimma matsayar fitar da hayaki ba tare da ƙarin ɗumamar yanayi ba nan da shekarar 2060, ba zai tabbata ba matuƙar ba a magance matsalolin mutanen da ke rayuwa a wuraren da ke cikin haɗari ba. Ya ce hakan ya yi daidai da muradin ci gaba mai ɗorewa na Majalisar Ɗinkin Duniya mai lamba 11, wanda ya mayar da hankali kan samar da birane da al’ummomi masu ɗorewa.
A cewarsa, yawancin unguwannin awon igiyar suna kusa da wuraren da ruwa ke taruwa da magudanan ruwa, yayin da ba su da isassun abubuwan more rayuwa. Ya ce mutanen da suka shafe shekaru suna fuskantar ambaliyar ruwa suna da muhimmiyar masaniya da za a iya amfani da ita wajen nemo hanyoyin magance matsalar. Haka kuma, ya bayyana muhimmancin gudunmawar mata wajen haɗa kan al’umma domin tsaftace magudanan ruwa, da kuma rawar da matasa ke takawa wajen amfani da fasaha wajen gano matsalolin muhalli.
Shugaban sashen ya ce taron zai bai wa malamai, masu tsara manufofi, abokan hulɗar ci gaba da sauran masu ruwa da tsaki damar musayar ilimi da gogewa, tare da samar da hanyoyin magance matsalolin muhalli. Ya buƙaci mahalarta su wuce matakin tattaunawa kawai, su samar da sakamako na zahiri, ciki har da ƙarfafa bincike da haɗin gwiwa da kuma samar da shawarwarin da za su taimaka wajen sauya manufofin gwamnati da ayyukan hukumomin bayar da tallafi.
A nasa jawabin, nataimakin shugaban Jami’ar Baba Ahmed da ke Kano, Farfesa Adamu Idris Tanko, ya ce taron na da matuƙar muhimmanci, saboda sauyin yanayi yana da alaƙa kai tsaye da yadda mutane ke rayuwa da kuma hanyoyin da suke dogaro da su wajen samun abin rayuwa. Ya nuna damuwa kan yadda unguwannin awon igiyar ke ƙaruwa cikin sauri ba tare da isassun hanyoyi, magudanan ruwa da ingantaccen tsarin gine-gine ba, yana mai cewa hakan na iya ƙara tsananta illolin ambaliyar ruwa da sauran bala’o’in da sauyin yanayi ke haifarwa.
Da yake wakiltar Mataimakin Shugaban Jami’ar Bayero, Farfesa Haruna Musa, Mataimakin Shugaban Jami’ar mai kula da harkokin ilimi, Farfesa Ahmed Muhammad Tsauni, ya ce al’ummomin Kano da sauran sassan Arewacin Najeriya sun fara fuskantar matsanancin zafi, ambaliyar ruwa, sauyin yanayin damina, ƙarancin ruwa da lalacewar muhalli. Ya ce saboda haka ya zama dole a haɗa matakan jure sauyin yanayi da tsara birane, rage talauci, kula da lafiyar jama’a, kare hanyoyin samun abin dogaro da kuma tabbatar da cewa kowa na da damar shiga cikin ayyukan ci gaba. Ya kuma yi kira da a ƙara haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, jami’o’i, al’umma da kamfanoni masu zaman kansu, tare da amfani da fasaha, bayanan tauraron ɗan Adam da nazarin bayanai wajen hasashen haɗari da samar da gargadin farko, ba tare da yin watsi da ilimin gargajiya da gogewar al’umma ba.
Shugaban kwamitin shirya taron, Farfesa Sani Ali, ya ce an samu takardun bincike sama da 60 daga mahalarta taron, waɗanda wasu suka gabatar da su kai tsaye, yayin da wasu suka shiga ta kafar intanet. Ya ce binciken ya shafi fannoni da dama, ciki har da yaƙi da sauyin yanayi, matsugunan da ba a tsara su ba, sa ido kan muhalli, jinsi, shugabanci, ɗorewar ci gaba da kirkire-kirkire. Ya bayyana fatansa cewa tattaunawar za ta ƙarfafa binciken ilimi, ta taimaka wajen tsara manufofin gwamnati, tare da samar da shawarwarin da za su taimaka wajen gina al’ummomi masu aminci, lafiya da kuma iya jure wa matsalolin sauyin yanayi.
