Ranar Hausa ta duniya: Sarakuna da masana sun nemi kare harshen Hausa

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe

Manyan baƙi da masu ruwa da tsaki a harkar raya harshen Hausa sun jaddada muhimmancin kare harshen da al’adun Hausawa, tare da kira ga al’umma, musamman matasa, da su rungumi harshen domin tabbatar da ɗorewarsa a wannan zamani na fasahar sadarwa.

Sun bayyana hakan ne a wajen bikin Ranar Hausa ta duniya, wanda ya haɗa manyan baƙi daga ciki da wajen Jihar Kano, ciki har da sarakuna, malamai, masana da shugabannin al’umma masu ruwa da tsaki wajen bunƙasa harshen Hausa da kare al’adun Hausawa.

Da yake gabatar da jawabinsa, Mai Martaba Ambasada Alhaji Ibrahim Haruna, Sarkin Hausawan Tukulma kuma shugaban majalisan masarauta Arewarmu duniyarmu African Chiefdom and Council, wanda wakilinsa, Ambasada Dr Usman Abubakar IPPS, CON, Ɗan Adalan Karaye, Ciroman Arewa kuma Wazirin Afrika, ya wakilta, ya ce harshen Hausa ba hanyar sadarwa ce kawai ba, illa wani muhimmin ginshiƙin tarihi, al’ada, ilimi da kasuwanci na al’ummar Hausawa.

Alhaji Ibrahim Haruna ya ce wajibi ne a bai wa harshen kulawar da ta dace, musamman ta hanyar ƙarfafa koyar da shi ga matasa da kuma amfani da shi wajen ilimi da fasahar zamani.

Sarkin ya yi kira ga sarakuna, shugabannin gargajiya, malamai, masana, matasa da mata da su haɗa kai wajen bunƙasa harshen Hausa da kare kyawawan al’adun Hausawa daga ɓacewa.

Ya kuma buƙaci al’ummar Hausawa da su shiga harkokin siyasa cikin mutunci, haƙuri da fahimtar juna, yana mai cewa bai kamata siyasa ta zama sanadin zagi, cin mutunci, ƙiyayya ko tayar da hankalin jama’a ba.

A cewarsa, ya kamata ‘yan siyasa su nemi ƙuri’un jama’a ta hanyar bayyana manufofinsu da abin da suke da niyyar yi wa al’umma, tare da mutunta ra’ayoyin juna da kuma karbar sakamakon zaɓen cikin lumana.

A nasa ɓangaren, wani mahalarci, Danjuma Usman, ya bayyana bikin a matsayin wani muhimmin mataki na tallata harshen Hausa da kuma nuna kyawawan al’adun Bahaushe.

Ya ce irin waɗannan bukukuwa na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da cewa harshen Hausa da al’adun Hausawa ba su gushe ba, musamman a tsakanin matasa.

Ɗanjuma ya yaba wa waɗanda suka shirya taron, yana mai cewa abin farin ciki ne ganin yadda ake ƙoƙarin ɗaga darajar harshen Hausa duk da ƙalubalen da yake fuskanta a wannan zamani.

Taron ya samu halartar manyan baƙi daga Kano da sauran sassan ƙasar, da kuma masu ruwa da tsaki da ke fafutukar kare harshen Hausa, tarihinsa da al’adunsa.

Mahalarta taron sun bayyana fatansu na ganin an ƙara faɗaɗa irin waɗannan shirye-shirye domin bunƙasa harshen Hausa da tabbatar da ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen haɗa kan al’umma da kuma yaɗa al’adun Hausawa a Afirka.

By ukarofi

Leave a Reply