Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Jihar Katsina ta karɓi katan 700 na ɗan ƙwamaso (RUTF) daga Ƙungiyar Red Cross ta Najeriya, domin tallafa wa ƙoƙarin gwamnati na yaƙi da tamowa, a tsakanin yara.
An miƙa kayan ta hannun Kungiyar reshen Jihar Katsina.
Za a rarraba ga yaran da ke fama da tamowa a faɗin jihar, tare da tabbatar da cewa kayan sun isa ga waɗanda aka tanada kuma an yi amfani da su yadda ya kamata.
Wannan ba shi ne karon farko da Red Cross ke tallafa wa Katsina wajen yaƙi da tamowa ba. A irin wannan lokaci a shekarar 2025, ƙungiyar ta bai wa jihar katan 1,144 na RUTF.
Gwamnatin Katsina ta yaba da tallafin Red Cross da sauran abokan hulɗarta, tana mai cewa irin waɗannan tallafe-tallafen na taimakawa wajen kare rayuwar yara da rage illolin tamowa a jihar.
