
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Tace Finafinai da Bidiyo ta Ƙasa (NFVCB) ta ce za ta ɗauki matakin doka akan furodusoshin fim ɗin Living in Colors bisa shirin fitar da fim ɗin ba tare da sahalewar hukumar ba.
Living in Colors wani fim da aka yi akan wasu matasa su biyar da ke zama a gida ɗaya a Legas, sannan suka nemi cigaba da zaman daduro a tsakaninsu ba tare da la’akari da jinsi ba.
A wata sanarwa da Shugaban NFVC, Dakta Shuaibu Husseini ya fitar, hukumar ta koka kan yadda ba a gabatar mata da fim ɗin ba domin nazari da kuma tacewa. Ya ce, duk da cewa bai kalli cikakken fim ɗin ba, tallansa da ya kalla ya nuna cewa akwai ababen da suka shafi batsa a ciki da kuma kwaɗaitar da al’umma alaƙar jinsi ta maɗigo ko luwaɗi a cikinsa.
A cewarsa, rashin bai wa NFVCB damar yin aikinta ya saɓa wa doka ta yadda gudanar da shi acikin al’umma haramun ne a yanzu.
Shugaban ya kuma ce, tuni hukumar ta fara aikin ɗaukar matakin doka kan waɗanda suka shirya fim ɗin da kuma sinimar da aka shirya ƙaddamarwa a ƙarƙashinta. Kazalika, ya gargaɗi al’umma da suka ƙaurace wa finafinan da ba su samu lasisin aiki ba daga NFVCB domin guje wa faɗa wa tarkon doka.
