
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya umarci rundunonin soji, ‘yan sanda, hukumar tsaro ta farin kaya DSS da sauran hukumomin tsaro da na leƙen asiri, da su gaggauta ƙaddamar da atisayen ceto mutanen nan masu yawa da aka sace a Jihar Neja.
Wannan umarni na zuwa ne bayan garkuwa da halaka wasu fararen hula daga ɓangaren ‘yan ta’adda a jihar, inda shugaban ƙasar ya koka akan aukuwar iftila’in.
A wata sanarwa da Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya fitar a ranar Talata, Shugaban ya bayyana masu hannu a mummunan harin a matsayin maƙiya zaman lafiya da tausayi, waɗanda ba za su guje wa fuskantar hukuncin doka ba.
Haka kuma, Tinubu ya miƙa saƙonsa na jajenta ga iyalan waɗanda aka halaka a yayin harin da kuma fatan samun juriyan rashin waɗanda aka halaka. Ya tabbatar wa iyalan waɗanda aka sace cewa gwamnati tana aiki tuƙuru wajen ganin an ceto baki ɗaya ‘yan uwan nasu.
Kazalika, Shugaba Tinubu ya umarci jagororin tsaro da su riƙa bayar da ba’asi kan halin da ake ciki na atisayen ceto har sai ta tabbata waɗanda abin ya shafa sun kuɓuta daga hannun ‘yan bindigar.
Har ila yau, gwamnatin tarayyar ta jaddada aniyarta ta bai wa rayuka da dukiyoyin al’umma kariya tare da tabbatar wa iyalan waɗanda abin ya shafa cewa za ta cigaba da ƙoƙari har sai an yi nasara kan al’amarin.
