
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An buƙaci Fadar Shugaban Ƙasa ta sake nazari akan haɗin mamban kwamitin yaƙin neman zaɓen APC a 2027 ne saboda waɗansu dalilai da ka iya tozarta yaƙin neman zaɓen, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
An yi ta cece-kuce daga ciki da wajen jam’iyyar tun bayan fitar da jaddawalin a ranar Asabar, inda da dama suka riƙa ankararwa kan cire wasu sunaye da sanya wasu da ake da alamar tambaya akansu.
A jaddawalin, an naɗa Shugaba Tinubu a matsayin shugaba da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima a matsayin maitaimaki. Haka kuma, an naɗa Shugaban APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda a matsayin mataimakin shugaba yayin tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari kuma aka ba shi muƙamin darakta-janar na kwamitin.
Wasu majiyoyi sun shaida wa Daily Trust cewa fadar shugaban ƙasar ta hanzarta zurfafa nazari kan jaddawalin ne ganin yadda ya ƙunshi kurakurai da dama akan haɗin da aka yi wa kwamitin zaɓen.
Daga cikin ababen da suka janyo tayar da jijiyar wuyan akwai sanya sunayen wasu jami’an gwamnati da waɗanda ma sun fuskanci zarge-zargen rashawa yayin da suke riƙe da madafun iko.
A wani labarin kuwa, Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar, Felix Morka, ya bayyana rahotannin da ke cewa fadar ta janye jaddawalin kwamitin yaƙin neman zaɓen APC a matsayin jita-jita, inda ya ce dukkan wani hukuncin da aka yanke kan kwamitin, za a ji shi ne daga bakin jam’iyyar a hukumance. Da yake magana a safiyar ranar Talata, Morka ya ce APC ba ta janye jaddawalin ba kuma ra rahotannin da ake yaɗawa akan haka ba gaskiya ba ne don haka jama’a su ƙaurace masa.
“Jita-jita ba labari ba ne. Idan mutane suan ɗaukar jita-jita, wannan ba labari ba ne. Akwai labarin bogi, sannan akwai labari na gaskiya,” inji Morka. A cewarsa, jam’iyyar za ta fitar da jawabi a hukumance muddin aka samu buƙatar yi wa jaddawalin wata kwaskwarima.
Hakan na zuwa ne bayan yaɗuwar wasu rahotanni a ranar Litinin da ke cewa wai jam’iyyar ta janye jaddawalin kwamitin yaƙin neman zaɓenta domin yin nazari a kai, yayin da aka koka kan waɗansu sunaye acikinsa.
