
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Siyasa, Kabiru Ibrahim Masari, sun bayar da tallafin jimillar Naira miliyan 600 domin gina jami’ar Fortune University.
Ƙungiyar Jama’atu Izalatul Bid’ah Wa’iƙamatus Sunnah (JIBWIS), reshen Jos ce ta samar da jami’ar a yankin Magama Gumau da ke Ƙaramar Hukumar Toron Jihar Bauchi, wadda ake aikinta tun a baya.
Masari da Gwamna Buni sun sanar da tallafin ne a ranar Lahadi yayin wani taron wayar da kan al’umma kan shiga harkar siyasa na kwana ɗaya mai taken “Enhanced Political Participation and Social Justice as a Panacea for Unity and Development in Nigeria”, wanda aka gudanar a Jos ƙarƙashin jagorancin JIBWIS.
Da yake jawabi a taron, Kabiru Masari ya ce, “Ban san cewa ƙungiyar tana gudanar da aikin ba. Don hakan na yi alƙawarin bada miliyan N300. Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe shi ma ya yi alƙawarin miliyan N300 a matsayin tallafin aikin.”
Da fari, Shugaban Majalisar Malamai na Ƙasa Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya yi kira ga al’ummar Musulmi a sassan Nijeriya da su bayar da gudunmawarsu domin gina jami’ar. Ya ce, da zarar an kammala aikin, makarantar za ta amfana da Musulmi da Kirista, don haka ba iya mabiya addinin Islama za a karɓa ba har ma Kiristoci da wasu na da damar shiga.
Haka kuma, malamin ya yi kira ga ɗaiɗaikun mutane da ‘yan siyasa da suka yi alƙawari da su yi ƙoƙari su cika domin ciyar da aikin gaba. Ya bayyana cewa, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barack Jibrin da Gwamnan Sakkwato, Ahmed Aliyu sun yi alƙawarin bayar da N450m da N300m.
Sheikh Jingir dai yana fuskantar suka kan yadda ƙarara yake bayyana goyon bayansa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, inda wasu ke zarginsa akan amfani da tasirin addini don cimma manufar siyasa ta hanyar kira ga zaɓar Musulmi da Musulmi a matakin shugabancin ƙasa.
