Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Hon. Ibrahim Osabwa darakta janar na ƙungiyar yaƙin neman zaɓe ta Injiniya Ishaq Dauda Elayo wato ɗan takarar kujerar sanata na Nasarawa ta Kudu ƙarƙashin jam’iyyar African Democratic Congress ADC yace ubangidan na sa shi ne ɗan takara da ya dace da zai bai wa mutanen yankin mazaɓar Kudancin jihar wakilci nagari mai ma’ana da magance matsalolin cigaba da ke fuskantar yankin.
Osabwa ya bayyana haka ne a wata hira na musamman da ya yi da ‘yan jarida a Keana. Yace Injiniya Elayo ya amsa kiran al’ummar yankin da suka daɗe suna kira gare shi da ya fito ya yi musu hidima a majalisar ƙasa ne.
Daraktan na yaƙin neman zaɓen Hon Ibrahim Osabwa yace babban abin da ya sa suka zaɓe shi, shi ne taimakon jin ƙai da yake yi tun da daɗewa da kuma kulawarsa ga marasa ƙarfi a faɗin al’ummomi a jihar. Ya bayyana ɗan takarar nasa a matsayin mutumin da yake nuna tausayi da jajircewa wajen inganta rayuwar talakawa ba tare da la’akari da asali ko ƙabila ba.
Osabwa ya kuma bayyana ƙwarewar ayyukan Elayo a matsayin babbar dama. Yace a matsayinsa na injiniya ya riƙa gudanar da ayyukan hanyoyi da dama a jihar Nasarawa dama jihohin maƙwabta ciki har da ayyuka da ya yi da Bankin Duniya ya ɗauki nauyi. Ya kawo misalin aikin hanyar Akwanga da Lafia da Makurdi haɗe da Enugu da aka yi a gwamnatin tsohon shugaba Muhammadu Buhari.
A cewarsa ƙwarewar Elayo a harkar bunƙasa ababen more rayuwa ta kuma ba shi ilimin da ya dace domin fahimta da magance wasu daga cikin manyan matsalolin da Nasarawa ta Kudu ke fuskanta. Saboda haka yace ɗan takararsa ya fi kowa tsayi a cikin ‘yan takarar kujerar sanata.
Shugaban ya ƙaryata rahotannin da ke yawo cewa Injiniya Elayo na shirin janyewa ya ba wani ɗan takara inda yace hakan ƙaryabce kuma ya jaddada cewa gogan nasa yana tsaye tsayin daka a takarar kuma ya ƙuduri aniyar neman goyon bayan al’ummar Nasarawa ta Kudu ƙarƙashin tutar ADC ɗin.
Da yake kuma bayyana abin da ya kira “tsarin cigaban Elayo”, Osabwa yace tsarin zai mayar da hankali kan buɗe ƙofar cigaban tattalin arziki da sanya Nasarawa ta Kudu ta zama wurin zuba jari. Ya lissafa hanyoyi da wutar lantarki da ruwan sha a matsayin manyan ababen more rayuwa guda uku da za su samu kulawa ta gaggawa idan Injiniyan yayi nasara.
Ya bayyana cewa inganta hanyoyi zai ƙarfafa kasuwanci da bunƙasa harkar noma da kuma sauƙaƙa zirga-zirgar mutane da kaya. Wutar lantarki mai ɗorewa kuma za ta tallafa wa ‘yan kasuwa da bunƙasa masana’antu da tallafa wa harkar fasaha da zamani. Ya ƙara da cewa samar da ruwan sha za a ba shi fifiko domin lafiyar al’umma mai amfani.
Osabwa ya ƙara da cewa tsarin da suka tsara zai kuma mayar da hankali kan koyar da sana’a da bunƙasa kasuwanci da ƙirƙire-ƙirƙire da kuma shirye-shiryen ƙarfafawa matasa da mata kana yace hangen nesan yaƙin neman zaɓen su ya haɗa da wakilci daga al’umma da samar da hanyoyin da ‘yan ƙasa za su iya isar da koke-koken su da kuma tabbatar da lissafi tsakanin ɗan majalisa da masu zaɓen sa.
Saboda haka yayi kira na musamman ga mazauna Nasarawa ta Kudu da su yi zaɓe da hankali su kuma goyi bayan Injiniya Ishaq Dauda Elayo.
“Ina kira ga mutane mu duba gaskiya mu wuce hayaniyar siyasa. Ina kira ga ‘yan yankin mu haɗa kai mu goyi bayan Elayo ɗan takarar da zai iya ceton mu daga wahala da matsalolin cigaban da ke addabar yankin sanatanmu,” inji shi.
