Gwamnatin Zamfara ta umarci sarakunan gargajiya su gabatar da ra’ayoyin jama’arsu kan kasafin kuɗin 2027

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Ma’aikatar kasafin kuɗi da tsare-tsare ta Jihar Zamfara ta ƙaddamar da shirye-shirye don kimanta kasafin kuɗi na shekarar 2027 tare a taron masu ruwa da tsaki, inda ta yi kira ga majalisun masarautu da sarakunan gargajiya da su gabatar da ra’ayoyin al’ummar su a ranar Juma’a ko kafin Juma’a, 4 ga Satumba, 2026.

Taron, wanda aka gudanar a ranar Talata a kwalejin fasaha da kimiyya (ZACAS) da ke Gusau, an yi masa taken “Shirye-shirye a yau, gina Zamfara mai albarka gobe.”

Da yake buɗe taron, kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare, Farfesa Yahaya Zakari, ya ce aikin ya nuna jajircewar gwamnatin Gwamna Dauda Lawal wajen gudanar da shugabanci bisa gaskiya da riƙon amana.

“Kasafin kuɗi shine tsarin da gwamnati ke aiwatarwa domin gudanar da ayyukan cigaba da suka shafi inganta rayuwar alumma” in ji Farfesa Zakari.

Ya lura cewa kasafin kuɗin da aka yi bisa ga ‘yan ƙasa shine mafi kyawun tsari da ke inganta rayuwar al’umma a duniya baki ɗaya.

“Lokacin da ‘yan ƙasa suka shiga bai wa gwamnati shawarwari, kasafin kuɗi yana samar da ainihin buƙatun su, yana inganta gaskiya, da kuma ƙarfafa riƙon amana,” in ji shi.

Kwamishinan ya bayyana wasu dandali guda huɗu da ‘yan ƙasa da cibiyoyi za su iya shiga cikin tsarin kasafin kuɗi, ciki har da hukumomin gwamnati, taro na zaure a kowanne gari, tattaunawa kan kasafin kuɗi na ƙasashe da kuma sauraron ƙorafin jama’a a majalisar dokokin Jihar Zamfara.

Farfesa Zakari ya buƙaci mahalarta taron da su mayar da hankali kan muhimman buƙatun al’umma, waɗanda suka haɗa da zaman lafiya da tsaro, Ilimi, lafiya, noma, kayayyakin more rayuwa, samar da ruwa, ƙarfafawa matasa da mata da ayyukan jin daɗi.

Ya bayyana cewa kasafin kuɗin 2027 zai ba da fifiko ga tsaro, noma, walwalar zamantakewa da ci gaban tattalin arziki a matsayin manyan abubuwan da ke haifar da ci gaba mai ɗorewa da rage talauci a jihar.

“Ina kira ga dukkan Majalisun Masarautu da su aika da buƙatunsu ga ma’aikatar kasafin kuɗi da tsare tsare a ranar Juma’a ko kafin Juma’a, 4 ga Satumba, 2026, don ba wa ofishin fasaha damar haɗa cikakkun bayanai don gabatarwar cikin kasafin kuɗin shekarar 2027.” in ji shi.

Farfesa Zakari ya ƙara bayyana cewa babban manufar wannan taron ita ce don tsara dabarun ci gaba mai ɗorewa da kuma rarraba albarkatu masu inganci don samun tasiri mai kyau ga rayuwar alumma da cigaban tattalin arzikin jihar.

By ukarofi

Leave a Reply